✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karin wa’adi: Jam’iyya ce ke da maganar karshe ba Buhari ba- APC

Jam’iyyar APC ta shaida wa kotu cewa a maganar karin wa’adin shugabannin jam’iyyar, ba Buhari ba ne ke da maganar karshe, domin kuwa jam’iyyar ce…

Jam’iyyar APC ta shaida wa kotu cewa a maganar karin wa’adin shugabannin jam’iyyar, ba Buhari ba ne ke da maganar karshe, domin kuwa jam’iyyar ce za ta zauna ta tattauna yadda za ta yi kuma shi ma dan jam’iyya ne kamar sauran ‘yan jam’iyyar.

Da ake zaman kotun, lauya masu kara Jibrin Okutepa (SAN) ya bukaci kotun da ta saurari shari’ar tunda shi kan shi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa karin wa’adin da aka yi ba daidai bane, kuma ya saba wa kundin tsarin jam’iyyar.

A nasa bangaren kuma, lauyan wadanda ake kara wato jam’iyyar ke nan, Akin Olujimi (SAN) da Joseph Daudu (SAN) da James Onoja (SAN) da Idris Yakubu (SAN) sun bukaci kotu ta dage sauraron kara zuwa wani lokaci domin su samu dama su amsa tambayoyin da aka musu.

Da yake martani a kan maganar Shugaban Kasa, Daudu cewa ya yi wannan ra’ayin shi ne kawai, sannan ba dole bane ya zama magana ta karshe. “maganar Shugaban Kasa Buhari ba dole ba ne a yi amfani da ita har sai jam’iyya ta zauna. Idan ana maganar jam’iyya. Shi ma kan shi dan jam’iyya ne kamar kowa.”