✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Karin kumallon ’yan Najeriya bayan yajin aikin gidajen burodi

Tsada da karancin burodi sun sa mutane sauya salon karin kumallo

’Yan Najeriya sun bayyana damuwarsu bayan yajin aiki da masu gidajen burodi suka shiga yajin a fadin kasar kan tsadar kayan hadi.

Masu sayen burodi sun bayyana cewa yajin gidajen burodi ya shafi rayuwarsu, musamman yanayin karin kumallonsu.

Wani mazaunin Abuja, Abba ya koka bisa karancin burodi da yajin aikin ya hadda, wanda da ya sa dole ya koma sayen kosai da masa a matsayin abin karin kumallo.

Mudi Wada, mazaunin rukunin Gidajen Kado a Abuja, ya ce yajin aikin gidajen burodin da tashin gwauron zabonsa sun tilasta iyalinsa amfani da wasu abubuwa domin kairn kumallo.

Kungiyar masu gidajen burodi ta Najeriya ta ce tsadar kayan hadi ta sa mambonin sama da 5,000 a fadin kasar sun karye, wasu dubban kuma na kokarin yadda za ci gaba da sana’ar a wannan yanayi.

Sakataren kungiyar na Jihar Kaduna, Musa Zamzam, ya ce yajin aikin nasu ba wai don tsadar kayan hadi ba ne kadai.

Ya ce har da rashin fitar da kudaden tallafin gidauniyar habaka noman rogo da gwamnatin tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ta kafa a shekarar 2012.

Ya ce, “Muna tambayar gwamnati game da kashi 15 cikin 100 da kwastam ke karba tana tura wa Babban Bankin Najeriya (CBN). Har yanzu taruwa kudaden suke yi.”

Masu gidajen burodin sun bayyana damuwa cewa yajin aikin nasu zai shafi haifar da rashin aikin yi, domin bangaren ne na biyu wajen yawan ma’aikata mutum sama da 450,000 a fadin Najeriya.

Kungiyar ta shiga yi yajin aikin gargadi na kwana hudu bayan ta bayyana damuwa ciki har da yawan harajin da gwamnati ke karba a hannun mamboninta.