✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘karin kudin ruwa zai shafi tattalinn arzikin Najeriya’

Shugaban kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Ma’adanai da kuma Aikin Gona ta kasa (NACCIMA) Cif Bassey Edem ya ce kara kudin ruwa da…

Shugaban kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu da Ma’adanai da kuma Aikin Gona ta kasa (NACCIMA) Cif Bassey Edem ya ce kara kudin ruwa da aka yi zai sa da wuya tattalin arzikin kasar nan ya fita daga halin da yake ciki.
A makon jiya ne Kwamitin da ke Kula da Kudi na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kara kudin ruwa daga kashi 12 cikin 100 zuwa 14.
Cif Edem wanda ya gana da manema labarai a Jihar Legas a karshen makon jiya, ya ce rage kudin ruwan zai taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin kasar nan.
“Kamar yadda muka bukaci kwamitin ya bunkasa sauran hanyoyin samun kudin shigar gwamnati, hakan ya sa za mu kara jan hankalin gwamnati na cewa za ta iya taimakon masu ruwa da tsaki ne a wannan harkar ta hanyar sauko da kudin ruwa, ”inji shi.
A karshe ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara duba manufofinta kan kasuwannin musayar kudin kasashen ketare musamman ganin yadda hakan ke shafar masana’antu.