Shugaban Rukunonin Kamfanin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya soki karin kuɗin ruwa da kimanin kashi 30 da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi.
Alhaji Aliko Ɗangote ya yi wannan suka ce a ranar Talatar da ta gabata a Babban Ɗakin Taro na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, lokacin fara taron wuni uku da Ƙungiyar Masu Masana’antu ta Nijeriya (MAN) ta shirya.
Attajirin Afirkan ya ce da wannan karin kuɗin ruwa abu ne mai wahala masana’antu su iya samar da aikin yi ko su bunkasa har su yi goyayya da saura.
- ‘Kula da marayu nauyi ne a kan al’umma’
- Gwamnatin Tarayya za ta maka Daily Trust a kotu kan rahoton Samoa
A taron Kwamitin Kuɗi na Bankin CBN (MPC) na karshe ya kara kuɗin ruwa da bankuna ke ɗorawa a kan basussukan da suke bayarwa a karo na uku a jere daga kashi 24.75 zuwa kashi 26.25.
An kara kuɗin ruwan da maki 400 zuwa kashi 24.75 daga kashi 18.75 a Fabrariru.
Sannan aka kara da maki 200 zuwa kashi 24.75 a watan Maris sai maki 150 zuwa kashi 26.75 a taron Kwamitin MPC na watan Mayu, inda Gwamnan CBN Olayemi Cardoso ya ce babbar manufar ita ce “A cimma daidaituwar farashi ta hanyar amfani da hanyoyin da ke ga mahukuntan harkokin kuɗi na dakile hauhawar farashin kayayyaki.”
A bayan nan Bankin Duniya ya gargaɗi Bankin CBN cewa ba zai iya hana hauhawar farashin kayayyaki ba ta hanyar karin kuɗin ruwa ba, wadda ya ce tana barazana ga bunkasar tattalin arziki.
Da yake tofa albarkacin bakinsa a yayin buɗe taron Aliko Ɗangote ya yi kiran a samar da sababbin tsare-tsare da za su kare masana’antun cikin gida, inda ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta kare harkokin kasuwanci da ake da su a kasar nan musamman masana’antu ta hanyar samar musu da yanayin da ya dace don bunkasarsu.
Ya ce, “Babu wanda zai iya samar da aikin yi da kuɗin ruwa kashi 30 cikin 100. Kuma bunkasar masana’antun ba za ta samu ba.
“Wajibi ne mu dubi kasashen da suka ci gaba a Yammaci da Gabashin Turai, waɗanda suka tsaye wajen kare masana’antunsu na gida.
“Dogaro da shigo da kayayyaki daidai yake da shigo da talauci da fitar da ayyukan yi zuwa kasashen waje. Babu wutar lantarki babu ci gaba, babu makoma mai kyau.
Har wa yau babu wadatattun kuɗaɗe babu ci gaba, babu kyakkyawar makoma. Babu yadda za a samu bunkasar masana’antu ba tare da ba su kariya ba.
Watsi da waɗannan abubuwa shi yake jawo rashin tsaro da ayyukan ’yan bindiga da garkuwa da mutane da bakin talauci,” ya nanata.
Alhaji Aliko Ɗangote ya ce samar da maasana’ntu ita ce “mafita kwaya ɗaya” ta ɗorewa da tsoma jama’a a harkokin tattalin arziki da bunkasa rayuwar ɗan Adam.
Ya kara da cewa, masna’antu za su ci gaba da kasancewa manyan hanyoyin bunkasa tattalin arziki da dogaro da kai.
“A fili yake cewa karfi masana’antun kowace kasa na nuna matsayinta na yin goyayya a harkokin kasuwanci a duniya, kuma kashi 70 cikin 100 suna samuwa ne daga kayayyakin da aka sana’anta.
“Ina sane da cewa Cibiyar Bretton Woods Institutions ta ruɗar da wasu masana tattalin arzikinmu a kan kalmar ‘kariya’ ta yadda wasu daga cikinsu suke tunanin kamar cin zarafin addini ne – wata kalma da ba za a furta ba a kamfani mai kyau.
To amma yaya aka yi China da Koriya da Indiya da sauran kasashen Asiya suka zamo masu karfin tattalin arziki har suke barazana ga manyan kasashe masu juya tattalin arzikin duniya?”
“Ana yawan gaya mana cewa bai wa masana’antunku kariya zai sa kasarku ta kasa gasa. Wannan shifcin-gizo ne.
“Hakika hakan ne ya fi dacewa. Na sha faɗin cewa ba za ka iya gasa ba, sai ka kare tare da tallafa wa masana’antunka.
“Don haka ina sake nanata cewa Nijeriya tana da duk abin da ake bukata ta bunkasa kuma ta ci gaba da gasa da masana’antun sauran kasashen duniya.
“Amma wajen yin haka wajibi ne mu sake tunani kan tsaretsaren masana’antunmu. Mu dubi kasashen da suke sahun gaba a Yamma da Gabashin Turai waɗanda da gaske suke yi wajen kare masana’antunsu na cikin gida.
“Mu ma waji ne mu kafa dokokin da za sukare masana’antunmu na cikin gida mu raine su don su girma su samu nasarar da za su samar da ayyukan yi da makoma mai kyau da muke matukar bukata,” in ji shi.
Da yake jawabi a wajen taron Shugaban Ƙungiyar MAN, Otunba Francis Meshioye ya ce yanayin da kanananharkokin tattalin arziki suke ciki na matukar illata ɓangaren masana’antu.
“Wannan yana matukar shafar aiki da hanyoyin rayuwar jama’a,” in ji shi. Ya ce babban taron an shirya shi ne don duba dalilan da suke kawo cikas ga bunkasar ɓangaren masana’antu “tare da yin tunani da samun matsaya da gwamnati kan abin da za a yi a magance su.”
Ya ce, “Babban burin taron shi ne sake fasalin ɓangaren ya haifar da ci gaba, kuma ya karfafa gasa da samar da ribar da za ta amfani tattalin arziki da kuma jin daɗin ’yan kasa.”
A jawabin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bukaci a fifita amfani da kayayyakin da aka yi a gida Nijeriya.
Ya kuma nuna rashin jin daɗinsa kan yadda masana’antun waɗanda suka kamata su taka muhimmiyar rawa wajen gina kasa ta hanyar sarrafa ɗimbin kayayyakin da ake da su, sai ga shi suna fama da koma-baya a shekara da shekaru.
Ya yi kira ga masu ruwa-da-tsaki su yi amfani da taron wajen samar da wata hanya da dabarun aiki da suka dace wajen aiwatarwa don kawo canji a ɓangaren masana’antun.
“Ya kamata mu sani ba za mu samu ci gaban kirki ba a kokarinmu na bunkasa samar da masana’antu har sai mu fifita samar da muhimman kayayyaki.
“Wajibi ne mu mayar da hankali wajen faɗaɗa sana’anta kayayyaki da fifita amfani da su tare da tallata kayayyakin da ake sana’antawa a Nijeriya.
“Ina tabbatar muku Dokar Shugaban Ƙasa ta 003- Tana goyon bayan fifita sayen kayayyakin da aka yi a cikin gida daga Gwamnatin Tarayya wajen fifita amfani da kayayyakin da aka yi a cikin gida – har yanzu tana aiki. An umarci ma’aikatu da hukumomin gwamnati da lallai su yi aiki da dokar,” in ji shi.