✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Karin haraji zai rage basukan da ake bin Najeriya —Minista

Ministar Kudi da Kasafi, Zainab Ahmed, ta ce karin haraji shi ne hanya mafi inganci na samun kudaden biyan basukan da ake bin Najeriya.

Ministar Kudi da Kasafi, Zainab Ahmed, ta ce karin haraji shi ne hanya mafi inganci na samun kudaden biyan basukan da ake bin Najeriya.

Hanya ta biyu, a cewarta, ita ce amfani da ingantattun dabarun toshe kofofin da ake karkatar da kudaden harajin daga aljihun gwamnati.

“Idan muka samu karin kudaden haraji, aka yi amfani da su yadda ya kama, za mu rage nauyin bashin da ke kan kasar nan,” in ji ta.

Ministar ta yi wannan kira ne a taron kara wa juna sani kan haraji da Hukumar ECOWAS ta shiryar kan hanyoyin tafiyar da haraji na bai-daya a kasashen kungiyar ECOWAS.

Ministar, wadda ta samu wakilcin Darektar Gudanarwar Ma’aikatar Kudi, Fatima Hayatu, ta ce, yadda ake gudanar da kudaden haraji ya zama babban abin damuwa ga gwamanti.

A watan Yuli Gwamantin Tarayya ta sanar cewa bashin da ake bin Najeriya ya kai tiriliyan N1.94 wanda yahaura kudaden shigar gwamanti da biliyan N310, a rubu’i na biyu na 2022.

Hakan na nufin kudaden shigar gwamnti sun gaza bashin da ake bin ta, ko da yake ministar ta ce yawan bashin bai haura abin da gwamanti ta kayyade wa kanta ba.

Ta ce, “Bashin ba abin da ba za a iya shawo kansa ba ne, gwamnati za ta toshe duk wasu kofofi da ake amfani da su wajen karkatar da kudaden haraji.

“Idan aka toshe su, aka koma yin komai a fili, za a samu karin kudaden yin ayyuka,” a cewar ministar.

Ta ce, inganta tsare-tsafiyar da haraji na samun karbuwa a Najeriya, kuma ana horar ga da jami’ai da kuman yin sauye-sauye domin samun nasarar hukumomin da nauyin ya rataya a wuyansu.