✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karfe 5 za a yi jana’izar Sarkin Zazzau – El-Rufai

Gwamna Nasir El-Rufai ya ce da karfe 5 za a yi jana'izar Sarkin Zazzau

Gwamna Nasir Ahmed El-Rufai na Jihar Kaduna ya ce da karfe 5.00 na yamma za a yi jana’izar marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.

Gwamnan ya bayyana haka ne bayan ya ziyarci asibitin da Sarkin ya rasu.

“Ina alhinin tabbatar da rasuwar uban jiharmu, Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Dokta Shehu Idris.

“Ya rasu ne a asibitin sojoji na 44 Military Reference Hospital da ke Kaduna yau (Lahadi) bayan gajeruwar jinya.

“In Allah Ya yarda za a yi jana’izarsa da karfe 5 na yamma”, inji gwamnan.

Mutane na ta tururuwa

Mutane na ta tururuwa zuwa Fadar Sarkin Zazzau (Hoto: Aliyu Babankarfi)

Ana sa ran Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar da sauran manyan sarakuna da jami’an gwamnati a matakai daban-daban za su hakarci jana’izar.

Sarkin na Zazzau dai ya rasu ne da karfe 12.00 na rana, kamar yadda Wazirin Zazzau Alhaji Ibrahim Aminu ya tabbatar wa Aminiya.

Tuni dai mutane suka fara tururuwa zuwa fadar Sarkin Zazzau don nuna alhininsu da mutuwar.

Marigayin, wanda daya ne daga sarakunan da suka fi dadewa a kan karaga a Najeriya, ya yi bikin cika shekara 45 yana mulki a watan Fabrairu.

Ya rasu yana da shekara 84 a duniya.