✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kare ya yi jana’izar dan uwansa

Wani kare ya zubar da hawaye tare da yin jana’izar dan uwansa  da ya mutu abayan mota ta buge shi. Tarihi na nuna cewa, shakuwar…

Wani kare ya zubar da hawaye tare da yin jana’izar dan uwansa  da ya mutu abayan mota ta buge shi.

Tarihi na nuna cewa, shakuwar abokantaka ta dan Adam da kare tana iya zama irin na jinsin halittar dabbobi biyu. Kare dai wani lokaci yakan shaku sosai da dan Adam kuma ya rika yin abin da mutum ke da muradi.

Kare yana kulla abota da kare dan uwansa. 

A nan wani bakin kare ne ke zubar da hawaye lokacin da abokinsa kare mai farin jiki ya mutu, alamar yana nuna bakin karen bai son mutuwar abokinsa ba, bayan ya fahimci lallai ya mutu ne sai ya fusata ya fara zubar da hawaye kamar zai dauke shi.

Bakin karen ya yi yunkurin ya ceto rayuwar abokinsa.