Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ga ci gaban mukalar da AbuMaryam AbdulRahman ya yi a kan iyayen da suke dora nauyi a kan ’ya’yansu mata da suke makarantun gaba da sakandare, ko kuma suke hidimar kasa. Muna fata za ku karanta don fa’idantuwa da darussan da ke cikinta.
Wasu abubuwa biyu da ke tabbatar mini da cewa, babu tantama irin wannan hali da iyaye ke yi na daga cikin abubuwan da ke sa da yawa daga ’yan matan da suka samu kansu a irin wannan halin shiga mummunar hanyar bin maza suna lalata da su, domin samun abin da za su rike kansu a irin wadannan makarantu, idan har ma kudin sun yi yawa a yi wa iyaye da kanne tsaraba ko wasu ma a rika ci da su.
Abu na farko da zan kafa hujja da shi shi ne, a wurin da nake kwadago a kan turo masu yi wa kasa hidima, an turo mana biyar, inda daya halinta ya bambanta da sauran ta wajen yawan rokon abubuwa a kusan kowane lokaci, kasancewar da dan abin da gwamnati ke ba su da kuma abin da muke ba su, ba su taka kara sun karya ba, amma sun isa su rike su zuwa wani lokaci, sai dai ita wannan kullum tana cikin rokon a ba ta kudi, ko a saya mata wani abu. Wani abin kuma shi ne, hatta shigarta ta saba da na sauran, kullum tana cikin kaya masu matse jiki, abin dai babu kan gado, ranar da dama ta samu sai tambaye ta cikin wasa, ko ita jikan moraka ce? Sai ta ce mini wallahi ba zan gane ba; matsalolin da take ciki ne suka sa dole sai ta hada da wasu abubuwa, domin ta yi daidai da irin bukatun da ke kanta, da bayanin ya yi nisa sai na fahimci cewa tun da tana hidimar kasa ana biyan ta, sai iyayenta suka ce ita za ta rika ba su kudi, kuma ta dauki nauyin karatun kannenta, to don Allah nawa ake biyan wanda yake hidimar kasa da har za a dora masa irin wannan dawainiya? Ya kamata dai iyaye a sake tunani.
Abu na biyu kuwa shi ne, cikin Azumin da ya gabata ne a cikin irin filiyen sada zumunta na hadu da wata daliba daga kwalejin kimiyya da fasaha, a lokacin muna tattaunawa, sai ta fada mini cewa a yanzu da muke magana da ita ba ta da wani abu da idan ta kai azumin ranar za ta ci, to a irin wannan hali wane tunani ne kake zaton wanda ke cikin irin wannan hali zai shiga? Mace fa ba namiji ba, kuma a wani gari mai nesa da inda take, to me kuke tunanin zai iya faru? Ai duk hanyar da wadannan ’yan mata suka samu za su bi domin samun biyan bukatar halin da suke ciki, to laifi a kan wa kuma?
Irin wannan ke sa ka ga ’yan mata a manyan makarantu suna bin munanan hanyoyi domin gani sun biya wa kansu dukkan bukatunsu da kuma samun kammala karatunsu. Ga yunwa, ga karatu, ga tunanin bukatar iyaye, me zai biyo baya ban da bin dalibai maza da malamai tun da babu kudin da za a ba su, kuma rashin sukuni ya hana karatu shiga kwakwalwa, illa ta saki kanta a yi ta lalata da ita domin samun abin masarufi da za ta kai wa iyaye da kuma samun ganin ta gama karatunta, wannan bai zama tamkar ka yi kiwon dabba ba ne, sai ta girma ta kai lokacin da za ka fara amfana sai ka dauke ta ka kai dokar daji ka sake ta ka ce ta yi kiwo kuma ta kare kanta. Iyaye a yi hattara
Abdurrahman Abumaryam
07066741919
08029151115