✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Karatu a Faransa: Ganduje ya umarnci a sa ido kan tallafin dalibai

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya umarci hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta jihar ta sanya ido kan yadda tsarin biyan kudaden tallafin…

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya umarci hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta jihar ta sanya ido kan yadda tsarin biyan kudaden tallafin karatu ga daliban jihar da ke karatu a kasar Faransa.

Ganduje ya ba Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado, umarnin ne a ranar Litini, inda ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ga ta ware Naira miliyan 67, don biyan kudaden tallafin karatun ga daliban.

Tun da farko dai a watan Fabrairun bana, gwamnatin jihar ta biya wani bangare na kudaden tallafin karatun daliban kimanin Naira miliyan 100.

Daliban da ke karatu a Faransa na karkashin wani shiri na musayar dalibai da Gwamnatin Jihar Kanon ta kulla da gwamnatin Faransa kuma galibinsu malamai ne a jami’o’in jihar ke karatunsu na digiri na biyu da digirin digirgir a kasar ta Faransa.