✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karasa Zabe: Za mu samar da tsaro a Kano —’Yan sanda

INEC ta ba da tabbacin gudanar da sahihin zabe a wuraren da za a sake zabukan.

Rundunar ‘Yan sandan Kano ta ba wa mazauna jihar tabbacin samun isasshen tsaro a yayin zaben da za a gudanar a ranar 15 ga watan Afrilu.

Kwamishinan ‘Yan sandan jihar, CP Mamman Dauda ne ya bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan zaben da za a karasa, wanda aka gudanar a ofishin INEC da ke Kano.

Mamman Dauda wanda Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da ayyuka, Mu’azu Mohammad, ya wakilta, ya ce tuni ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro a jihar suka tsara yadda yanayin tsaro zai kasance a ranar da nufin tabbatar da zabe cikin kwanciyar hankali.

CP Dauda ya ce ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a jihar na kokarin ganin an gudanar da zabe ba tare da an samu wani rikici ba.

Ya bayyana cewa tuni aka ba da umarnin aiki kan yadda za a samar da tsaro a duk runfunan zabe ga jami’an da aka tura domin gudanar da aikin.

Kwamishinan ‘yan sandan ya shawarci shugabannin jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da su gargadi magoya bayansu da su guji yin duk wani abu da zai kawo tashin hankali kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe.

A nasa bangaren, Kwamishinan Zabe na jihar, Ambassada Abdu Zango, ya ce duk da cewa an gudanar da zabukan Shugaban Kasa da na gwamnoni cikin kwanciyar hankali a Kano, wasu mazabu na Tarayya da na jiha an samu kalubalen da ya sa za’a sake zaben.

Ya ce wasu daga cikin rumfunan zabe da abin ya shafa da za a sake gudanar da zaben sun hada da kananan hukumomin Danbatta da Makoda da Dawakin Tofa da Gabasawa da Gezawa.

Sauran sun hada da Gaya da Takai da Garko, da Wudil da Warawa da Ungogo da Ajingi da Gwarzo da Tudun Wada da Fagge.

Zango ya jaddada aniyar INEC na tabbatar da sahihin zabe a wuraren da za’a karasa zabukan.