Kankarar da ake sayarwa kan kudi Naira 30 guda daya kafin zuwan watan azumi, yanzu duk guda daya ta koma Naira 100 a cikin birnin Gombe.
Aminiyata yi bincike kan dalilin da ya haddasa tsadar kankarar da kuma ko masu sayarwar suna samun ribar da ya kamata saboda kukan da suka yi na cewa karancin wutar lantarki ya taimaka wajen tashin farashin nata.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 suna tsaka da bude-baki a masallacin Taraba
- DAGA LARABA: Barnar da ’yan bindiga suka yi a Arewa maso Yammacin Najeriya
Madam Mercy (Mama Ishaya), da ke saro kankarar ta kuma sayar, ta ce suna amfani da watan azumi ne suna sayo kankarar suna sayarwar suna dan samun abin da ya samu, don su samu abin da ba a rasa ba.
“Ba wuta a yanzu, inda muke saro kankarar dole su kara kudi, saboda da inji suke amfani su ma, shi yasa mu ma muke kara kudi don mu mayar da uwar kudin, sannan mu samu na rufawa kai asiri,” in ji ta.
Madam Mercy, ta ce suna saro manyan kankarar a kan Naira 100 su yi kudin mota sannan kuma su sayar a kan Naira 150, amma a hakan wata takan zama asara domin ta kan tsiyaye kafin su sayar, a karshe suna iya samun ribar Naira 20 ko 30 a kan kowacce kankara.
Ta ce hakan yana taimaka musu, ya fi su zauna ba sa yin komai, kuma ba don karancin wutar lantarki da kuma tsadar da ta yi ba, da za su iya samun riba fiye da yadda suke samu a yanzu.
Shi ma wani saurayi mai suna Ibrahim Adamu, mai sana’ar sayar da kankarar, cewa ya yi inda suke saro kankarar ne ake musu kukan tsadar katin kudin wuta, shi yasa ake sayar musu da ita da tsada.
Kazalika, ya ce a baya ba ta wuce Naira 10 zuwa 20 suke saya, su kuma su sayar a kan Naira 50 amma yanzu abun ba haka ya ke ba .
Wata mai gidan sayar da kankarar a unguwar BCGA da ke Gombe, Hajiya Maryam Musa, cewa ta yi tana sana’ar sayar da kankara shekara uku, amma ba su taba fuskantar tsadar ruwa da wutar lantarki irin na wannan lokacin ba.
Ta kuma ce ruwa ma da suke saya a tankuna ya kara kudi, ledar kulla ruwan ta yi tsada, bare uwa-uba wutar lantarki ta yi karanci ga kuma tsada, shi kuma janareto ba zai musu abin da suke so ba.
Wani magidanci mai sayan kankara yau da kullum, Garba Abu Baban Sadiq, ya ce a kullum yana sayan kankarar Naira 1,000 ko 700 a gidansa wanda a baya ba ta wuce ta Naira 500 zuwa 600 da ya ke saya ba.
“Wato gaskiya ana cikin wani hali, a bara kankarar dana ke saya ba ta wuce ta 600 baki daya, amma yanzu tana haura 1,000 ma,” a cewarsa.
Binciken Aminiya ya gano yadda wutar lantarki ta yi tsada, inda a da, da Naira 1,000 ‘units’ 32 ake samu a baya, yayin da a yanzu kuma ake samun units 16 kacal.