✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karancin takardun kudi: Gwamnonin APC 3 sun maka Buhari a kotu

Gwamnonin sun hada da na Kaduna da Kogida kuma Zamfara

Gwamnoni uku na jam’iyyar APC sun maka Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a gaban Kotun Koli kan sauya takardun kudin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi.

Gwamnonin sun hada da na Kaduna Nasir El-Rufai da na Kogi Yahaya Bello da kuma na Zamfara, Bello Matawalle.

Jihohin na neman kotun ta tabbatar da dokar da CBN ke aiwatarwa a halin yanzu bisa umarnin Shugaba Buhari cewa ta saba wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, da dokar Babban Bankin Najeriya ta 2007.

Gwamnonin sun kuma ce wa’adin da CBN ya bayar na daina karbar tsofaffin takardun kudin ya saba wa sashe na 20 (3) na dokar CBN na shekarar 2007, wanda ya  ce dole ne a bayar da isasshen lokaci kafin aiwatar da irin wannan manufa.

Babbar Lauyar Gwamnati, kuma Kwamishiniyar Shari’a ta Jihar Kaduna, Aisha Dikko, ta ce duk da cewa bullo da manufar sake fasalin Nairar an yi ta ne don karfafa tsarin Gwamnatin Tarayya na rage amfani da tsabar kudi, amma ba duk hada-hada ce ake yi ta wanna tsarin ba.

Aisha ta ce baya ga haka, tsarin an yi shi ne a takaitaccen lokaci, kuma hakan ya gurgunta rayuwar ’yan Najeriya da ita kanta gwamnatin, musamman ma sabbabin takardun kudin da suka yi matukar karanci har a bankuna.

“Al’ummar da suke karkara a jihohin masu kara, ba su da damar cire kudi ko musanya tsofaffin da ke hannunsu, saboda babu bankuna a yankunansu, ga shi su ne suka fi yawa a cikin al’umma,” in ji ta.

Ya zuwa lokacin hada rahoton nan dai, kotun ba ta sanya ranar fara sauraron karar ba.