An samu karancin zirga-zirgar ababen hawa a kan titunan Kano a sakamakon matsalar karancin man fetur da ke kara ta’azzara.
Wasu daga cikin mutanen da Aminiya ta zanta da su sun bayyana fargabarsu cewa ci gaban mastalar karancin man na iya haifar da tashin farashin kayan masarufi.
- DAGA LARABA: ‘Yadda Masu Kwacen Waya Suka Kashe Dan Uwana Bayan Sun Illata Ni’
- Zaluncin ’yan kasuwa ne ke kawo tsadar man fetur – Masu ababen hawa
Aminiya ta gano yawancin gidajen man fetur a Kano suna rufe, ’yan kalilan din da ke sayarwa a shake suke da mutane wadanda suke bin dogayen layuka don su samu man.
Masu bn layi a gidajen mai sun shaida mana cewa bayan wahalar da suke sha kafin su samu man, masu gidajen mai na cin karensu babu babbaka, inda kowanne ke sa farashi yadda yaga dama, maimakon farashin da gwamanti ta kayyade na NN163 a kan kowace lita.
Zuwa ranar Talata, a gidan man Audu Manager ana sayar da litar man a kan Naira 200. A gidan man Salbas kuma ana sayarwa a kan Naira 190.
Mutane da dama da suka tattauna da Aminiya sun nuna rashin jin dadinsu game da daukar tsawon lokaci da mutum yake yi a kan layin sayen man kafin ya kai ga samu.
Wani ma’aikacin gwamnati a Kano, Malam Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa ya kwashe awa biyu yana bin layi a gidan mai, kuma har zuwa wancan lokaci bai kai ga samu ba.
“Kasancewar ni ma’aikacin gwamnati ne ya sa na fito neman mai tun da sassafe da niyyar idan na samu man na koma gida na shirya na tafi wurin aiki; Amma kin ga har yanzu da na shafe tsawon awa biyu ban kai ga samun man ba, ballantana na tafi wajen aiki,” inji shi.
Barazanar iya kawo tsadar abinci
Har il yau, alummar jihar sun koka game da yadda karancin man ke kara ta’azzara a kullum, lamarin da suke tsoron zai iya janyo tashin farashin kayan abinci.
Malan Ado Ali ya bayyana cewa, “A yanzu tsoron da muke ji shi ne kada abin ya ci gaba har ya janyo a kara farashin kayan abinci. Dama ga shi a yanzu ana cikin wani hali da talaka yake kasa cin abinci sau uku saboda tsada.”
Shi kuma wani mai suna Malam Ya’u ya bayyana cewa, “Wannan karancin man fetur wasu shugabanni ne suka kirkire shi don su jefa rayuwar mutane cikin wahala baya ga wacce suke ciki tuntuni.”
Kasuwar ’yan bumburutu ta bude
Aminiya ta gano yadda a gefe guda lamarin na karancin man ya janyo kasuwar ’yan bunburutu ta bude inda suke sayar da man a kan farashin da suka ga dama.
Idris Ado, wani dan bumburutu ne da muka zanta da shi a Kano, ya bayyana cewa duk da cewa suna samun kudi sosai saboda karancin man, amma ba su goyon bayan a ci gaba da samun karancin man a fadin kasar nan.
“Gaskiya ne muna samun kudi sosai a wanann lokaci amma muna fatan a kawo karshen wannan matsala. Idan kin duba yawancin al’umma suna cikin matsala.”
‘Gidajen mai na matse famfo’
Sai dai su ma ’yan bunburutun sun koka game da yadda masu gidajen man ke matse famfam litarsu.
Wani mai suna Muhammad Zaharadden ya bayyana cewa, “Kudin litar man fetur din a yawancin gidajen man bai canza ba.
“Abin damuwarmu shi ne yadda ake matse famfon, inda ake samun litar man ba ta cika. Ba mu san me ya sa ba.”
Yawanicn mutanen sun nemi gwamnati da ta yi duk me yiyuwa wajen ganin ta magance wannan matsala ta karancin man fetur da ta ki ci, ta ki cinyewa.