✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Karamar Sallah da ladubbanta

Abubuwan da ya kamata a aikata ranar Idin Karamar Sallah.

A yayin da al’ummar Musulmi suka kammala Azumin Ramadan, Karamar Sallah za ta kasance a ranar Alhamis a Najeriya.

Ga kuma ladubban da malamai suka kwadaitar a aikata da Karamar Sallah, ranar farin ciki da godiya ga Allah bisa ni’imominsa da kammala azumin Ramadan:

Kabbarori:

Ana bukatar Musulmi su rika yin kabbarori daga ranar da aka ga watan Shawwal har zuwa lokacin da za a tayar da Sallar Idi a ranar Sallar.

Abin da ake so shi ne yin kabbarorin a bayyane, kuma akwai siffofi da dama.

Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar la ilaha illal Lah, Allahu Akbar Allahu Akbar walil Lahil hamd, daya ne daga cikin siffofin yin kabborin.

Zakatul Fitr:

Hadisi ya nuna fitar da Zakkar Kono farilla ne ga mai hali waibi ne a lokacin Karamar Sallah, a ba wa miskinai.

Za fitar wa kansa sannan sauran wadanda nauyin ciyar da su ke kansa, kowane mutum daya cikin Sa’i daya (Mudun Nabi hudu).

Ana iya fitarwa tun kwana uku kafin ranar Sallah, amma wajibcinta na farawa ne daga ranar Sallah.

Ana bayarwa ne kafin a tafi sallar idi, wanda ya bayar kuma bayan sallar idi, to ta zama sadaka kamar sauran sakakoki.

Wankan Idi:

Malamai sun ce Mustahabbi ne mutum yin wankan ibada kafin zuwa sallar idi a ranar Sallah. Siffar wankan daya ce da sauran wankan ibada.

An tambayi Ali bn Abi Dalib (RA) game da wanka sai ya ce, “Ana yi a ranakun Juma’a, Arafa, Karamar Sallah da Babbar Sallah.”

Sabbin kaya:

Mai zuwa idi, ana bukatar ya sanya sabbin tufafi, idan babu, sai ya sa kayansa mafiya kyau.

Hadisin Ibn Abbas (RA) ya ce Manzon Allah na da wata jar alkyabba da yake sawa a ranar idin Karamar Sallah.

Imam Al-Bayhaki ya ruwaito cewa Ibn Umar kan sanya mafiya kyan kayansa a ranar idi.

Sabanin ranar Juma’a da ake bukatar mutum ya sanya fararen tufafi, abin da ake so a lokacin idi shi ne a sa wasu launuka na kaya.

Turare:

Ga maza, ana bukata su su kasance cikin ado, su sanya turare domin  tafiya masallacin idi.

Cin abinci:

Ranar Id ranar ci da sha ce, kuma Haramun ne a yi azumi a ranar. A Karamar Sallah ana so mutum ya ci abinci kafin tafiya idi.

Hadisi ya nuna Manzon Allah (SAW) kan ci dabino (adadin mara) a safiyar Karamar Sallah kafin fita zuwa idi. Wanda bai samu dabino zai iya cin wani abun.

Zuwa Sallar Idi:

An fi so mutum ya taka zuwa masallaci, a kan lokaci, yana tafiya, yana yin kabbarori.

Ana zuwa sallar idi tare kananan yara da mata har da masu jinin al’ada, sai dai su masu yin jinin al’adar za su kebe daga gefen sahu.

Babu kiran Sallah ko nafila

Ba a yi wa sallar idi kiran sallah sannan ba a yin nafila a wurin sallar idi. Zama kawai za a yi ana kabbarori a jira isowar liman.

Abdullahi bin Abbas ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya yi sallar Idi raka’a biyu, bai yi wata salla (ta nafila) kafinta ko bayanta ba.”

Jabir bin Abdullahi ya ruwaito Hadisi cewa, “Babu kiran sallah kafin ko bayan zuwan liman kuma babu ikama.”

Siffar Sallar Idi:

Duk da cewa Sallar Idi ba farilla ba ce, ana yin ta ne a jam’i. Raka’a biyu ce kamar kowace sallah mai raka’a biyu kuma a bayyane ake yin ta jim a lokacin Walha.

A raka’ar farko ana yin kabbarori shida bayan Kabbarar Harama. Raka’a ta biyu kuma ana yin kabbara biyar bayan kabbar mikewa zuwa raka’ar.

Sauraraon huduba:

A sallar idi liman kan gabatar da huduba ne bayan an idar da sallah.

Ana bukatar masallata su jira su saurari hudubar kuma laifi ne magana a yayin da liman ke huduba.

Hadisi ya nuna babban kuskure ne mutum ya ce wa wani ya bar magana a yayin da liman ke gabatar da huduba, ida ga shi mai maganar.

Taya murna:

Ana bukatar a yi wa juna murna da fatan alheri a ranar Sallar Idi.

Jubayr ibn Nufair ya ruwaito cewa Sahabbai kan yi wa junansu addu’ar Allah Ya karba musu ibadun da suka yi gabanin ranar.

Sauya hanya:

Sunna ce mutum ya sauya hanya idan zai koma gida daga sallar idi, kamar yadda Jabir bn Abdullah ya ruwaito Manzon Allah (SAW) ya yi a ranar idi.

Zumunci:

Sada zumunci na daga cikin abubuwan da ake bukata daga mutum ranar sallar idi.

Barka da Sallah!