✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

karamar Hukumar Nasarawa ta lashe kofin magoya bayan Kano Pillars

kungiyar Magoya Bayan Kano Pillars Reshen karamar Hukumar Nasarawa ce ta zama zakara&nbsp a gasar da aka shirya wa kungiyoyin kwallon kafa na magoya bayan…

kungiyar Magoya Bayan Kano Pillars Reshen karamar Hukumar Nasarawa ce ta zama zakara&nbsp a gasar da aka shirya wa kungiyoyin kwallon kafa na magoya bayan Kano Pillars da ke rassan kananan hukumomin Jihar Kano a gasar da&nbsp aka kammala a kwanan nan.
kungiyar reshen karamar Hukumar Nasarawa ta zama zakara ne bayan da ta doke karamar Hukumar Fagge da ci hudu da biyu ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida (fanariti) bayan da suka yi daya da daya&nbsp a minti casa’in din da suka yi suna buga wasa a wasan karshe a filin wasa na Knao Pillars da ke Sabon Garin Kano.
kungiyar karamar Hukumar Sumaila ce ta zama kungiya mafi da’a a gasar yayin da kuma mai horar da ‘yan wasan karamar Hukumar Nasarawa&nbsp Coach
Auwalu Asibiti ya samu kyautar mai horar da ‘yan wasa mafi kwazo. Daraktan wasanni na Jihar Kano Alhaji Bashir Ahmad Maizare ne ya wakilci Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Knao Alhaji Ibrahim Galadima a wajen rufe gasar.
A jawabinsa Shugaban Hukumar Gudanarwar kungiyar kwallaon kafa ta Kano Pillars Alhaji Kabiru Baita ya yaba wa wadanda suka shirya gasar tare da yin alkwarin yin aiki tare da duk wata kungiya ko wani mutum da suke da shirin kawo ci gaban kungiyar ta Kano Pillars a ciki da wajen Jihar Kano.
Haka kuma ya taya wadanda suka samu nasara murna tare da yin kira ga wadanda ba su samu nasarar ba da su dauki al’amarin a matsyain kaddara.
A jawabinsa Shugaban kungiyar Magoya Bayan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars&nbsp na Jihar Kano&nbsp