✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kar ku tada rikici a Najeriya saboda zabe —WAEF ga ’yan siyasa

Kungiyar Dattawan Afirka ta Yamma (WAEF) tayi kira ga ’yan siyasa da jam’iyyu da magoya bayansu, su ci gaba da zama lafiya bayan sanar da…

Kungiyar Dattawan Afirka ta Yamma (WAEF) tayi kira ga ’yan siyasa da jam’iyyu da magoya bayansu, su ci gaba da zama lafiya bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasa da ’yan majalisu.

Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Talata dauke da sa hannun wakilanta a Najeriya wato tsohon shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama, da na Najeriya Goodluck Jonathan.

Kungiyar ta ce duk wanda bai gamsu da sakamakon zaben ba, ya yi amfani da hanyoyin da doka ta ba shi dama don shigar da korafinsa.

“Muna fatan cimma kudurorinmu a Najeriya, har zuwa lokacin da za a kammala harkokin zaben kasar.

“Kuma muna amfani da wannan dama don yin kira ga al’umma da su zauna lafiya, su kuma bi doka,” a cewar sanarwar.

WAEF ta kuma yaba wa ’yan Najeriya bisa nuna kishin kasar da suka yi ranar Asabar, na fitowa kwansu da kwarkwata don kada kuri’a cikin lumana.