Kungiyar Dillalan Mai ta Najeriya (IPMAN) ta umarci gidajen mai kar su kara farashin litar man fetur daga Naira 143.
IPMAN ta ce su jira umarnin hukumar kayyade farshin mai (PPPRA) da ta kara Naira shida a farashin sarin mai daga dafo-dafo daga N132.62 zuwa N138.62
Da yake magana kan karin, kakakin IPMAN, Suleiman Yakubu, ya ce kungiyar za ta sanar da zarar ta samu umarnin PPPRA ka sabon farashin.
A ranar Talata Hukumar Sayar a Albarkatun Mai (PPMC) ta sanar da karshin farashin wanda ya fara aiki daga Laraba 5 ga Agusta, 2020.
Amma Yakubu ya umarci gidajen mai da su sayar da shi a kan tsohon farashin har zuwa lokacin da PPPRA za ta sanar da nasu karin farashin.
Karo na uku ke nan cikin wata hudu da hukumar take sauya farahsin mai a Najeriya.
An kara farshi a Legas da Kano
Sai dai a zagayen da wakilin Aminiya ya yi a Legas, wasu gidajen mai har sun kara farashin, inda suke sayar da litar fetur a kan N148.62.
A jihar Kano kuma, shugaban IPMAN reshen jihar, Bashir Danmalam ya umarci gidajen mai da su fara sayar da litar fetur a kan N150.
Ya bayyana cewa hakan ya biyo bayan sabon karin da gwamnati ta yi a farashin man.
Amma a zagayen da wakilinmu ya yi a sassan Abuja ya gano cewa yanzu gidajen mai ba su kara farashi daga yadda suka saba sayarwa ba.