✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kar a zabi masu ikirarin an saya musu tikitin takara —Obasanjo

Matsalar Najeriya ta ta’allaka ne ga shugabanci mai rauni.

Tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya gargadi ’yan Najeriya a kan kada su zabi duk wani dan takarar shugabancin kasar da ya yi ikirarin cewa wasu ne suka saya masa tikitin tsayawa takara.

RFI ya ruwaito Obasanjo na wannan jawabi ne a yayin wani taro a Lagos, inda ya ce matsalar Najeriya ta ta’allaka ne ga shugabanci mai rauni.

Obasanjo ya bayyana takaici ganin yadda ’yan takara ke ikirarin cewa matasa ne suka tara naira miliyan 40 don saya musu tikitin yin takara, yana mai kira a gare su da kada su yi wa al’umma karya.

Tsohon shugaban Najeriyan ya ce za a iya shawo kan matsalolin da suka addabi kasar ne kawai ta wajen samar da shugabanci mai inganci, inda ya ce Najeriya na bukatar canjin shugabanci a halin yanzu.

Bayanai sun ce tsohon shugaban Najeriya Atiku Abubakar; tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki; Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sakkwato da tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi na daga cikin ’yan takara a karkashin inuwar jam’iyar PDP  da suka yi ikirari cewa wasu ne suka saya musu fom din bayyana kudirin tsayawa takara.