✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kar a yi la’akari da jam’iyya ko addini a Zaben 2023 —Sanusi II

Ya yi kira da a duba cancanta wajen zaben shugabanni a babban zaben 2023.

Khalifan Tijjaniya na Najeriya, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a duba cancanta wajen zaben shugabanni na gari a babban zaben kasa na 2023 da ke tafe.

Aminiya ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya ya yi wannan kira ne a wajen taron shekara-shekara na tunawa da ranar haihuwar Manzon Tsira, Annabi Muhammad (SAW) da aka gudanar a Lakwaja, babban birnin Jihar Kogi.

Sarkin Kano na 14 ya yi gargadin cewa kar a yi la’akari da akida ta jam’iyya ko addini wajen zaben shugabanni, inda ya yi kira da a fi karkata kan wadanda ake kyautata musu zaton za su fidda kasar nan zuwa tudun mun tsira.

A kan haka ne ya bukaci wadanda suka cancanci kada kuri’a da su mallaki katin zaben gabanin babban zaben na badi.

Sanusi ya sake nanata muhimmanci jama’a su zabi shugabanni na gari ba tare da la’akari da siyasa ko addini ba.

“Idan matasanmu suka samu aikin yi, tattalin arzikin kasar baki daya zai inganta.

“Mafi mahimmanci, mu ba jam’iyya ba ce, amma ba za mu iya nade hannayenmu mu yi watsi da siyasa ba,” in ji shi.

“Duk dan Tijjaniya daga shekara 18 zuwa sama namiji ko mace ya je ya mallaki katin zabe.

“Allah yana umurtar mu da mu dogara da shugabannin da muka aminta da riko da gaskiyarsu.

“Yanzu muna wani lokaci da jama’a ne ke da ikon nada shugabanni, kuri’arku ita ce karfin ku, kuna da nauyi a kanku’’ a cewar Muhammadu Sanusi II.

“Ba wai ina kira ba ne a kan dole sai an zabi ’yan Tijjaniya, ko Musulmi ko wata jam’iyyar, amma ya zama tilas mu yi iyaka kokarinmu wajen zaben shugabannin da suka cancanta.

“Kuma duk wanda bai sauke wannan nauyin da rataya a wuyansa ba, ya ci amanar addinin Musulunci.

“Dole ne mu tsaya tsayin daka wajen kare martaba da hadin kan kasar nan domin mu samu ’yanci a fannin karatu, ilimi da kuma zaman lafiya.”