Manoma a Najeriya sun ce shirin Gwamnatin Tarayya na bude iyakokin kasar na kan tudu a daidai lokacin da farashin kaya suka yi tashin gwauron zabi na da hadarin gaske.
Sun ce muddin aka bude iyakokin, kasashe masu dogara da Najeriya wurin sayen abinci da sauran bukatu za su yi mata tsinke domin sayayya, kuma hakan zai kawo karin tsadar kaya.
- Yadda Najeriya za ta fita daga matsin tattalin arziki — Ministar Kudi
- An yi garkuwa da iyalan dogarin Atiku
- Ganduje zai dauke Gidan Zoo daga Kano
Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta ce nan ba da jimawa ba Shugaba Buhari zai karbi rahoton kwamitin da ya kafa ya ba shi shawara kan bude iyakokin da aka rufe.
“Ya kafa kwamitin da nake jagoranta tare da ministocin harkokin waje, cikin gida, hukumar kwastam, hukumar shige da fice, da hukumomin tsaro domin yin nazari mu kuma ba shi shawara kan rufe iyakar.
“Kwamitin ya kammala aikin kuma zai mika rahoton, na riga na sa hannu na kuma mika wa kowa ya sa hannu tsakanin yau zuwa gobe don mu mika wa Shugaban Kasa”, inji ta.
Bayanin ministar bayan taron Majalisar Zartarwa ta Kasa (FEC) ranar Laraba ya sa ’yan Najeriya zaton nan ba da jimawa ba za a bude iyakokin da aka rufe tun a watan Agustan 2019.
Najeriya ta rufe iyakokinta a lokacin ne bisa zargin fasakwaurin makamai, kwayoyi da kayan abinci zuwa cikin kasarta daga makwabtanta da sauran sassan duniya.
Najeriya ita ce mafi karfin tattalin arziki a cikin kasashen Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) mai mambobi 15.
Jamhuriyar Nijar, Chadi, Benin da Kamaru masu iyaka da Najeriya sun dogara da ita ne sosai domin samun wasu bukatunsu.
Rufe iyakar ta gurgunta harkokin kasuwancin miliyoyoin ’yan kasar da kan ci gajiyar kusanci tsakanin kasashen domin neman abin dogaro.
Matakin da Najeriya ta dauka ya haifar da damuwa a kasashen har ma da Ghana, saboda harkokin tattalin arzikinsu sun samu koma-baya.
Amma da take bayani, Minista Zainab, ta ce kwamitin nata zai yi wa Buhari bayanin alfano ko rashin alfanon rufe iyakokin da aka yi.
A jawabinta bayan taron Majalisar Zartarwa ta Kasa, ta ce da zarar kwamitin ya rattaba hannu a kan rahoton za su mika shi ga Buhari.
Sai dai kuma ba ta ce uffan ba game da ranar da za su mika rahoton ga Shugaban Kasa ba ko lokacin da za a bude iyakokin.
A lokacin wata tattaunawa a Taron Tattalin Arziki na Kasa na 26 (NES #26) ta ba da tabbaci cewa za a bude iyakokin nan ba da jimawa ba.
Ta ce: “Shugaban Kasa ya kafa kwamiti kuma mun yi nazari, mun amince muna kuma ba Shugaban Kasa shawara lokaci ya yi a bude iyakokin.
“An cimma manufar saboda a cikin watannin mun samu mun yi aiki da kawayenmu a wani kwamiti mai rassa uku, muka yi sintirin hadin gwiwa a kan iyakoki tare da jaddada alkawarin da ke tsakaninmu.
“Kowane bangare ya koyi darasi kuma abin da Najeriya ta yi yana shafar kasuwanci a kasashen yadda ita ma yake shafar ta a cikin gida.
Don haka muke sa ran za a bude iyakokin nan ba da jimawa ba amma Shugaban Kasa ne zai zabi lokacin”, ta shaida wa taron.
Rufe iyakokin ya yi daidai —AFAN
Shugaban Kungiyar Manoma ta Kasa (AFAN) Arch. Kabiru Ibrahim, ya shaida wa Aminiya cewa yawancin kayan abincin da ake samarwa a Najeriya na zurarewa zuwa kasashen makwabta, don haka bude iyakokin zai saukaka wa masu yin haka ci gaba da ayyukansu.
“Manoma na samar da abinci amma farashi sai tashi yake yi saboda wasu dalilai.
“To me kake tunani idan aka bude iyakokin aka bari a yi hada-hadar kayayyakin zuwa kasashen makwabta? Abin zai kazance”, inji shi.
Ya ja hankalin masu neman a bude iyakokin game da sake bullar cutar COVID-19, yana mai cewa matakin zai haifar da karin matsaloli.
Bude iyakoki zai kassara manomna —Minista
A baya-bayan nan, Ministan Noma, Muhammad Sabo Nanono, ya bayyana adawarsa ga bude iyakokin, wanda ya ce zai yi illa ga manoma.
A wata hira ta musamman da Aminiya, ministan ya ce bude iyakokin zai gurunta nasarar da aka samu a kokarin samar da isasshen abinci a kasa.
Muna amfana da rufe boda —Kananan manoma
Kananan manoma na cikin gida sun ce duk da cewa rufe iyakokin ya kawo tsadar wasu kaya a kasar, rufewar ta fi musu amfani.
Mallam Nuhu Ayuba manomin shinkafa ne, ya shawarci gwamnati ta yi hattara domin bude iyakokin a yanzu zai rusa ribar sadaukar da kai da ’yan Najeriya suka yi.
“Mun san farashin kaya sun tashi kuma hakan abin damuwa ne, amma muddin so muke mu wadata kasa da abinci, to dole mu hakura mu bar iyakokin a rufe a halin yanzu”, inji manomin shinkafar.
Masu kiwon kaji na so a bude boda
Amma wani mai kiwon kaji, Mista John Shagbaya, ya ba da shawarar a bude iyakokin na wucin gadi don su samu saukin matsalar da bangaren noman kaji ke fuskanta.
“Farashin masara da waken soya sun karu wanda ke nufin na cikin gida ba zai wadace mu ba.
“A bude iyakokin ko da na dan lokaci ne saboda a shigo da waken soya da masara domin a samu saukin farashin abincin tsuntsayen”, inji shi.
Babu kasar da za ta rayu da rufe iyaka
Shugaban Hukumar Kasuwanci da Raya Masana’antu ta Abuja (ACCI), Prince Adetokumbo Kayode, ya ce matakin rufe iyakokin kuskure ne da gwamnati ta yi ba tare da tuntubar ’yan kasuwa ba.
A cewarsa rufe iyakokin ya gurgunta tattalin arzikin Najeriya sosai, don haka ya bukaci gwamnati ta gaggauta sake shawara ta bude iyakokin.
Shugaban na ACCI ya ce rufe iyakokin “mataki ne na wucin gadi da aka dauka cikin gaggawa” ba tare da zurfafa tunani ba.
“Mu a iya saninmu, ba a yi tunani mai zurfi ne saboda gwamnati bata tunbubi ’yan kasuwa masu amfani da iyakokin ba.
“Gwamnati ta dau matakin ne sannan ta ba da hujjarta, ba tare da sanin cewa farashin mai zai karye ko COVID-19 za ta dagula al’amura ba”, inji shi.
Ya ce a baya gwamnati ta so ta bude iyakokin amma bullar annobar COVID-19 ya sa dole ta dakatar da yin hakan.
“Babu shawarar da ba a yi kuskure a cikinta kuma babu wata gwamnati da ba ta kuskure, saboda haka idan aka yi kuskure a yarda an yi.
Ya ci gaba da cewa: “Idan aka makale a cikin rami yadda za a fita ake nema ba ci gaba da hakawa za a yi ba. Ina rokon Shugaban Kasa ya gaggauta bude iyakokin”.
Ya ce yarjejeniyar kasuwanci babu shamaki tsakanin kasashen Afirka AfCFTA da Najeriya ta sanya hannu a kai ya isa zama dalili ta bude iyakokin.
Prince Kayode ya ce Najeriya ce jagora a harkar kasuwanci a fadin yankin Afirka ta Yamma.
“Bai kamata mu rufe iyakokinmu ba alhali mu ke jan ragamar kashi 90 zuwa 95 na kasuwanci a Yammacin Afirka. Gaskiyar zancen ke nan”.
Shi ma Shugaban Hukumar Kasuwanci da Raya Masana’antu ta Legas (LCCI), Muda Yusuf, ya ce bude iyakokin shi ne abin da ya dace.
A cewarsa, hakan zai taimaka wa kokarin da ake yi na farfado da tattalin arzikin Najeriya daga durkushewar da ya yi.
Duk da haka ya bukaci a karfafa samar da tsaro a kan iyakokin kasashen.
“Aikin gwamnati shi ne tabbatar da bin dokoki da tsare-tsare. Matsalar da muka fara samu ita ce gazawar gwamnati, yawancin hukumomi na ba da kai bori ya hau.
“Ya kamata a yi wa tsarin karbar kudaden shiga garambalul domin cimma manufar.
“Mu ci gajiyar girman kasa da albarkatun Najeriya a matsayin babbar cibiyar tattalin arziki a Yammacin Afirka”.
Darakta-Janar din na LCCI ya ce bude iyakokin shi ne abin da ya dace idan aka yi la’akari da yarjejeniyar AfCFTA da aka kulla da Najeriya.
Mai sharhi a kan harkokin kudi kuma Manajan Daraktan Kairos Capital da ke Legas, Sam Chidoka, ya ce bude iyakokin shi ne abun da ya fi dacewa.
“Rufewa iyakokin ya gurgunta hada-hadar kasuwanci da fitar da kaya ta iyakokin kan tudu”, inji Chidoka.
Masanin ya ce rufe iyakokin ya sa hauwawara farashin kayan abinci ya yi tsanani kuma bude su na iya sawa a samu sauki.
Ya ce rufe iyakar ta sa Najeriya ba ta iya shigo da kayan da take bukata, don haka ba za ta iya samar da wasu kaya a cikin gida ba sakamakon karancin kayan da kuma tsadar farashi.
“Idan aka bude iyakokin, makwabtamnu za su samu damar yin kasuwanci da mu saboda babu kasar da za ta rayu ita kadai.
“Ana maganar yin fasa kwauri, amma gaskiyar ita ce ba ta iyakokin da ake sintiri ake shigo da wadannan haramtattun kaya ba”, a cewarsa.
Ya ci gaba da cewa: “Gwamnatin ta yi dukkan mai yiwuwa domin ganin hukumomin da ke da alhakin tsare iyakokin kasa suna yin aikinsu”.