A ranar Larabar makon jiya ce kanwar Marigayi Rashidi Yekini shahararren dan kwallon Najeriya mai suna Rofiat Yekini ta rasa ranta a wani hadarin mota da ya rusta da ita a kan hanyar Okuku zuwa Osogbo.
Rahotanni sun nuna kanwar tasa da ke da ’ya’ya uku ta rasu ne a nan take tare da wadansu mutane biyu a motar da ke dauke da fasinjoji 18. An ce motar tasu ta yi taho-mu-gama ce da wata motar dakon kaya.
A lokacin da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Lauyan da ke kare iyalan Rashidi Yekini mai suna Barista Mohammed Jubril ya ce hadarin ya rutsa da Rofiat ce a lokacin da take kokarin komawa garin Offa bayan ta ziyarci wata kasuwa a a kan hanyarta ta masaukinta a Offa. Ya ce al’amarin ya faru ne da misalin karfe daya na rana a ranar Larabar makon jiya.
Tuni aka yi jana’izar marigayiyar kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
kanwar Rashidi Yekini ta rasu a hadarin mota
A ranar Larabar makon jiya ce kanwar Marigayi Rashidi Yekini shahararren dan kwallon Najeriya mai suna Rofiat Yekini ta rasa ranta a wani hadarin mota…