✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kanu ya dauki nauyin yi wa yara hudu aiki a zuciya a kasar Indiya

A ranar 26 ga watan jiya ne (Disamba) Cibiyar Tallafawa Masu Matsala a Zuciya ta Kanu Heart Foundation ta dauki nauyin wadansu yara hudu da…

A ranar 26 ga watan jiya ne (Disamba) Cibiyar Tallafawa Masu Matsala a Zuciya ta Kanu Heart Foundation ta dauki nauyin wadansu yara hudu da ke da matsala a zuciya don tafiya Indiya wajen yi musu aiki.
Jama’a da dama sun ci gajiyar wannan cibiya ta Kanu inda cibiyar ta rika aika su sassan duniya tana daukar nauyinsu don ganin sun samu sauki daga matsalar zuciya.
“Mun aika wadansu yara hudu zuwa Indiya don a yi musu aiki a zuciya, don haka muna rokon addu’ar ’yan uwa da abokan arziki su taya su da addu’ar neman samun nasara a aikin da za a yi musu.  Yaran sun bar kasar nan ne a ranar 26 ga watan Disamban, 2013”,  kamar yadda Kanu Nwankwo ya sanar a wata takarda da ya fitar mai dauke da sanya hannunsa.
Nwankwo Kanu, mai kimanin shekara 37 a shekarar 1996 ce ya samu matsala a zuciya jim kadan bayan Najeriya ta lashe Lambar Zinare a bangaren kwallo a gasar wasannin Olamfik da aka yi  a Atlanta da ke Amurka da hakan ta sa sai da aka yi masa aiki.
Bayan ya samu sauki ne ya yanke shawarar kafa Cibiyar Tallafawa Marasa karfi wadanda suka samu matsala a zuciya kuma tun daga wancan lokaci ya zuwa yanzu cibiyar ta taimaka dubban mutane musamman matasa wadanda suka kamu da matsalar ciwon zuciya.
Tuni iyalan yaran suka roki Allah Ya saka wa Kanu da alheri a kan taimakon da ya yi musu na daukar nauyin yaransu zuwa Indiya don a yi musu aiki a zuciya.