Kungiyar zababbun kansiloli na Jam’iyyar APC a jihar Edo, sun gudanar da zanga-zangar lumana a kan rike musu albashin watanni biyar.
Kansilolin dai sun mamaye titin birnin Benin rike da allunan da ke dauke da rubutaccen fushinsu da suka hada da: “A biya mu albashin mu na watanni bakwai” da “ana zaluntarmu ne don mun ki koma wa PDP” da “Mu talakawa suka zabe mu” da dai sauransu.
A bayaninsa, Honorabul Emwinghare Osabuohien, wanda shi ya yi magana a matsayin shugaba, ya zargi gwamna Godwin Obaseki, da tsayar musu da albashi saboda sun ki binsa jam’iyyar PDP.
- Tsarin IPPIS: Buhari ya dakatar da biyan albashin lakcarori
- Tsarin IPPIS: Buhari ya dakatar da biyan albashin lakcarori
“Muna son duniya ta san cewar a matsayinmu na zababbun kansiloli na kananan hukumomi 16 cikin 18, mu sama da 90 ba a biya mu albashinmu ba tun daga wata Mayun 2020.”
“Haka kuma ba a biya mu duk wani alawus da wasu ‘yan kudade da ya kamata a biya mu ba.”
“Kuma Gwamna ya hana a biyamu don da muka tambayi Shugabannin Kananan Hukumomin sun ce mu je mu tambayi gwamna.”
“Laifin mu shi ne mun ki bin gwamna da ya sauya sheka, wanda mun san bai yi aiki ba saboda haka muka ki bin sa PDP.”
Osabuohien ya ce, “Bayan an hana shi takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC, ya ce mu duka mu bi shi jam’iyyar PDP, amma muka kiya.”
“Tun daga wannan lokacin ya sa a rike mana albashin mu, amma aka ci gaba da biyan ‘yan uwanmu da suka bi shi.”
Kansilolin kuma sun yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ’Yan Majalisar Tarayya da Oba na Benin da duk wani mai fada a ji, da su taimaka a kwato musu hakkinsu wajen Gwamnan.
A raddin da ya yi, mai magana da yawun Gwamna Obaseki, Crusoe Osagie, ya ce babu wanda ke bin gwamnati albashi ko wasu kudade.
Ya ce, gwamnatin jihar ba ta taba kin biyan wani ma’aikacinta albashin sa ba.
A cewarsa, “Gwamnatin jihar Edo na daya daga cikin jihohin da ba sa wasa da albashi ma’aikatansu, don haka cewar suna bin gwamnati albashi ba shi da tushe kuma zargin wai an ki biyansu saboda bambancin jam’iyyar siyasa ya fi muni.”
Wannan zargi ne na karya kuma ya kamata jama’a su yi watsi da shi,” in ji Osagie.