✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kansila ya ɗauki nauyin karatun marayu 120 a Kano

Kansilan ya ce zai ci gaba da bayar da wannan tallafi ko ba ya riƙe da kujerar siyasa.

Kansilan mazaɓar Achika da ke Ƙaramar Hukumar Wudil a Jihar Kano, Alhaji Bashir Aliyu, ya ɗauki nauyin karatun marayu 120 da ba sa zuwa makaranta a jihar.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa, yayin da yake gabatar da kayayyakin karatu ga marayun, ya ce ya ɗauki nauyin tallafa musu ne sakamakon rashin wanda zai tsaya musu wajen samun ilimi.

Ya ce matakin na da nufin inganta ilimi da kuma kyautata makomarsu idan sun girma.

Bashir, ya ce za a yi wa marayun rajista a ƙaramar sakandare ta gwamnati da kuma ƙaramar sakandare ta Larabci ta gwamnati da ke Achika.

Ya yi alƙawarin ɗaukar nauyin waɗanda suka ci gajiyar tallafin daga matakin ƙaramar sakandare har zuwa matakin babbar makarantar sakandare.

“Za a ci gaba da bayar da wannan tallafi ko da bayan na bar ofis,” in ji shi.

Kansilan ya ce hakan na daga cikin irin gudummawar zai bayar wajen ci gaban jihar.

“Na fi mayar da hankali kan tallafa wa masu rauni da masu ƙaramin ƙarfi,” in ji shi.

A cewarsa, shirin zai tabbatar da makomar yara da ba sa zuwa makaranta musamman marayu.

Bashir, ya ce waɗanda suka ci gajiyar sun haɗa da ’yan mata 65 da maza 54, inda ya ce kimamin 50 daga cikinsu sun daina zuwa makaranta gaba ɗaya.

“Zan ci gaba da kula da waɗannan yaran har sai sun kammala makarantar sakandare. Ƙarfafa wa yara irin waɗannan, waɗanda marayu ne, babbar hidima ce ga al’umma.

“Suna buƙatar goyon bayan al’umma don zama nagari kuma masu amfani a cikin al’umma. Yin watsi da su zai iya jefa su cikin hatsari.

“Shi ya sa na yanke shawarar ɗaukar nauyin karatunsu tun daga matakin ƙaramar sakandare har zuwa babba ko da ba na riƙe da wata kujerar siyasa,” in ji shi.

Daga cikin kayayyakin da aka raba wa marayun sun haɗa da litattafai 1,200, jakunkunan makaranta 120, kayan makaranta 240 da kuma takalman makaranta 120.

Ragowar sun haɗa da safa 120, alƙalamin rubutu 240 da kuma fensir guda 240.