Bayan da ya yi nasarar tara kudi dala miliyan daya a dandalin sada zumunta, tsohon dan wasan kungiyar Sevilla, Fred Oumar Kanoute, ya shirya gina wani babban masallaci a birnin Seville da ke kasar Spaniya wanda shi ne irinsa na farko a cikin shekaru 700.
Dan kasar Faransar wanda ya taka leda a kungiyar Sevilla a kasar ta Spaniya ya bayyana hakan ne ranar Talata.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter lokacin da ya ke nuna godiyarsa ga wadanda suka taimaka ya ce, “Ina godiya sannan ina fatan Allah Ya sakawa duk wanda ya taimaka a wannan gidauniyar”.
- Moses, Lacazette, Ighalo sun shiga tsaka mai wuya; Neymar zai ci gaba da zama a PSG
- Juventus na shirin gwanjon Pjanic, Costa da Higuain
Bayan masallacin dai, gidauniyar za ta kuma gina wata cibiyar al’adu wa al’ummar Musulmin da ke birnin.
Kanoute, wanda ya musulunta tun yana da shekara 20 a duniya, ya fada wa gidan talabijin na Al-Jazeera cewa lokacin da ya je birnin na Seville ya sha wahala sosai kafin ya samu masallaci.
“Lokacin da na je [Seville], akwai matukar wahala mutum ya samu masallaci; sai da na sha wahalar tambayar mutane”, inji shi.
Akwai sama da Musulmi 300,000 a birnin na Seville wadanda suka hada da Spaniyawa, da kuma ‘yan kasashen Algeria da Morocco da Senegal da Mali.
A shekarar 2017 Kanoute ya sayi wani fili wa Musulmin birnin inda za su ci gaba da gudanar da ibadunsu bayan kudin hayar wurin ya kare.
Kudurin nashi na yanzu dai zai bai wa al’ummar Musulmi a birnin wurin ibada da ba a yi irin shi ba tsawon lokaci.