Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta shirya tsaf don fara gudanar da gasar wasannin kwallon kafa da na hannu da wasannin motsa jiki a tsakanin kananan makarantun sakandaren da ke jihar.
Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano Alhaji Ibrahim Galadima ne ya bayyana haka a wajen taron da aka gudanar wanda ya kunshi kodineotocin wasanni na Ma’aikatar ilimi na shiyya-shiyya da shugabbannin da sakatarori na kungiyoyin wasanni da kuma masu horar da ’yan wasa.
Sai dai Shugaban Hukumar wasannin ya bayyana rashin jin dadinsa game da rashin halartar da yawa daga cikin kodinotocin wasanni wajen taron inda ya bayar da tabbacin daukar matakin da ya kamata don ganin an magance wannan mummunar dabi’a.
Da yake bayani game da dokokin gasar Shugaban Kwamitin Shirya gasar Farfesa Rabi’u Muhammad Chanhu ya bayyana cewa dalibai maza ne kadai za su buga wasannin kwallon kafa yayin da maza da mata za su taka rawa a sauran wasannin.