Laila Buhari ta samu wannan nasara ne a karo na shida ke nan da Laila Buhari take neman takarar dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kano ta Tsakiya, ba tare da ta kai labari ba.
“Ina godiya ga duk wadanda suka shiga aka dama da su musamman maboboin jam’iyyar PDP da suka tabbatar an yi abin da ya dace.
“Wannan babbar nasara ce, musamman ga matasa da mata,” kamar yadda Laila, wadda ta fara siyasa tun a 1981 ta bayyana.
Laila Buhari ta samu tikitin takarar ne a zaben fitar da ’yan takara da bangaren Sanata Bello Hayatu Gwarzo na PDP ya gudanar.
Zuwa yanzu, fitacciyar ’yar siyasar ta nemi takarar Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya a jam’iyyun NPN, UNCP, PDP, PSP, ACN da kuma APC.