✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kano ta Tsakiya: Kotun Koli ta tabbatar da takarar Laila Buhari

Kotun Koli ta sake tabbatar da Hajiya Laila Buhari a matsayin ’yar takarar Sanatan Kano ta tsakiya a Jam’iyyar PDP.

A ranar Alhamis Kotun Koli ta sake tabbatar da Hajiya Laila Buhari a matsayin ’yar takarar Sanatan Kano ta tsakiya a Jam’iyyar PDP.

Aminiya ta ruwaito cewa a baya kotun daukaka kara ta tabbatar da Laila Buhari inda kuma ta soke zaben Danburan Abubakar Nuhu.

Kotun kolin da ta yanke hukuncin da Mai Shari’a Muhammad Lawal Garba ya karanta, ta yi watsi da dukkan dalilan daukaka kara na Danburam Nuhu.

Mai Shari’a Garba na tare da Masu Shari’a Kudirat Kekere Ekun, da Saulawa da Ibrahim Jauro, da Emmanuel Agim.