✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano: Sarakunan Arewa sun buƙaci a zauna lafiya

Tuni masu ruwa da tsaki a Arewacin Najeriya suka fara kiranye-kiranye don neman a zauna lafiya.

Majalisar Sarakunan Arewa, ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III, ta yi kira da a samar da zaman lafiya biyo bayan rikicin masarauta da ya ɓarke a Jihar Kano.

Wannan dai na zuwa ne bayan rushe masarautu biyar da majalisar dokokin jihar ta yi tare da dawo da Alhaji Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

Bayan rushe masarautun, gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya bai wa sarakunan umarni miƙa al’amuran masarautunsu ga mataimakin gwamnan Jihar, Kwamared Aminu Abdulsalam.

Sai dai tsohon Sarkin birni, Alhaji Aminu Ado Bayero da aka tsige, ya dawo jihar tare da shiga ƙaramar fada da ke yankin Nassarawa a jihar, lamarin da ya haifar da ruɗani.

Da yake mayar da martani game da lamarin, Gwamna Yusuf ya bayar da umarnin kama Aminu Ado Bayero, amma ‘yan sanda suka bijire wa umarnin gwamnan, inda suka ce za su mutunta umarnin kotu.

Sarki Sanusi II na ci gaba da jan ragamar masarautar Kano daga babbar fada, yayin da Aminu Ado Bayero ke aiki daga ƙaramar fada da ke Nassarawa, sai dai hakan na ci gaba da haifar da ruɗani.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, gammayar malaman addinin Musulunci, ƙungiyoyi da sauransu, sun yi kira ga shugaba Bola Tinubu da ya sa baki kan rikicin masarautar da ke ƙara ƙamari a jihar.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, majalisar sarakunan ta yi kira da a yi sulhu.

“Majalisar ta yi kira ga ɓangarorin da ke rikicin da su yi sulhu don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali tun da lamarin na gaban kotu.

“Majalisar na addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki ya zaunar da Kano da ma Najeriya lafiya.”