Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce Hukumar Karbar Koke-koke da Hana Cin Hanci da Rashawa ta Jihar (PCACC) ce mafi jajircewa a Najeriya wajen kwato hakkin jama’a da tabbatar da shugabanci na gari.
Ganduje ya bayyana hakan ne yayin wani taro da Kungiyar Akantoci ta Najeriya (ANAN), wanda aka gudanar a Kano ranar Talata.
- Kano ta ba da aikin hanyar miliyan N500 a biliyan N1.4
- Rashawa: Babu Gawuna a binciken da muke yi -Muhuyi
- Hukumar yaki da cin hanci ta gargadi ’yan kasuwa a Kano
- Ganduje ne jagoran yaki da cin hanci a Najeriya —Salihu Tanko Yakasai
Ganduje ya ce, “A Kano muna da Cibiyar Yaki da Cin Hanci da Rashawa mai karfi. Aikin da hukumar ke yi ya sa wasu kwamishinoni, Daraktoci, Sakatarorin gwamnati sun rasa ayyukansu.
“Ma’aikatanmu na samun horo ne daga Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) da sauran hukumomin yaki da rashawa a matakin tarayya don su samu kwarewar zamani wajen yaki da cin hanci da rashawa”, inji shi.
Gwamnan ya kuma yaba wa ANAN, ya kuma karfafa mata guiwar ci gaba da kasancewa karkashin inuwar kungiya don samun cigaba mai dorewa.
A nasa jawabin, shugaban ANAN, Farfesa Muhammad Akaro Mainoma, ya yaba wa Gwamna Ganduje bisa yadda ya ce ya sauya Kano a mulkinsa.
Shugaban kungiyar ya kuma shaida wa mahalarta taron cewa za su samu horo ne bisa tsarin dokar gudanarwa, alkinta ayyukan jama’a, rahoton kudi, dabarar yaki da cin hanci na zmani, fasaha da kimiyyar ilimin akanta da dai sauransu.