✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano: Mun kama jami’inmu da ya ce mun janye daga daukaka karar Abba – INEC

INEC ta ce tuni ma ta kama jami'in da ya fitar da wasikar

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta musanta janyewa daga karar da Gwamnan Kano da jam’iyyarsa ta NNPP suka daukaka kan hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben Gwamnan Jihar.

Kwamishinan hukumar mai kula da wayar da kan jama’a, Sam Olumekun, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da maraicen Asabar a Abuja.

Aminiya ta rawaito yadda aka shiga rudani a Kano bayan bayyanar wata takarda daga hukumar da take nuna ta janye daga daukaka karar da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da kuma jam’iyyarsa ta NNPP suka yi kan hukuncin da ya soke nasararsu.

Wasikar, wacce ke dauke da kwanan watan 6 ga watan Oktoban 2023, mai dauke da sa hannun Shugaban Sashen Shari’a na hukumar a ofishinta na Kano, Suleiman Alkali, inda ta ce sun janye sakamakon ba su da dalilin daukaka karar.

Sai dai a cikin sanarwar da hedkwatar INEC ta fitar ta bakin Kwamishinan, ta nesanta kanta daga wasikar ta Kano, inda ta ce ba ta da tushe.

Sam ya ce, “Muna so mu bayyana karara cewa wannan wasikar ba ingantacciya ba ce. Tuni ma mun janye ta, kuma mun ma cafke jami’in.

“Saboda haka kuma muna kira ga jama’a da su dakatar da ci gaba yada cewa hukumar ta janye daga cikin karar, ko kuma ma abin da ya fi haka muni, cewa ta kyale shari’ar,” in ji Kwamishinan.

Ya ce a duk lokacin da mai shigar da kara ya saka hukumar a cikin shari’a, to dole ne ta shige ta kamar yadda ya bukata.

“A sakamakon haka, tuni mun umarci lauyoyinmu da su ci gaba da shiga shari’ar, kamar yadda dokokin da suka kafa ta suka tanada. Tsarin kuma yana nan a haka, bai canza ba,” in ji Sam.

A watan da ya gabata ne dai Kotun Sauraron Kararrakin Zabe da ke Kano ta soke nasarar Abba sannan ta ayyana Nasiru Yusuf Gawuna na APC a matsayin wanda ya lashe zaben. Sai dai tuni Abba ya daukaka kara yana kalubalantar hukuncin.