Hukuma da ke Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta jihar Kano (KAROTA) ta ce ta cafke wani matashi da ake zargi da yin sojan-gona da sunan hukumar ta hanyar kama ababen hawa ya ci tararsu da daddare.
Hukumar ta cafke matashin ne dai-dai lokacin da yake tsaka da tare motoci a kan titi da misalin karfe 12:00 na daren Litinin.
- Joe Biden ya rattaba hannu a kan dokar zubar da ciki a Amurka
- Ba mu da wani shafin Hausa in ba na Aminiya ba – Daily Trust
Matashin, mai suna Lukman Abdullahi, mai shekaru 27 mazaunin unguwar Sabon Gari bayan kama shi ya bayyana cewa shi dan Maiduguri ne da ke jihar Borno.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar ta KAROTA, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa ya raba wa manema labarai a Kano ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce matashin na amfani da kayan hukumar ne saboda jama’a su fahimci cewa shi ma’aikacinta ne.
Hukumar ta ce dama ta jima da samun rahoton yadda matashin yake amfani da sunanta wajen musguna wa al’umma, wanda sai a wannan karon dubunsa ta cika.
Daga karshe sanarwar ta ce Shugaban Hukumar ta KAROTA, Baffa Babba Dan-Agundi, ya shawarci al’umma da su ci gaba da kai rahoton duk wani jami’in da suka ga yana karbar cin-hanci domin ya fuskanci tuhuma a gaban kotu.
Nabilusi ya kara da cewa idan suka kammala binke a kansa za su mika shi hannun ’yan sanda domin fadada bincike tare da gurfanar da shi a gaban kotu domin fuskantar hukunci.