Mai magana da yawun Gwamnan Jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf na iko da ‘yancin cire ko naɗa duk wanda yake so a matsayin Sarki a jihar.
Dawakin Tofa, ya bayyana haka ne cikin hirarsa da gidan talabijin na Arise a ranar Asabar.
- An ɗaure matashi shekara 1 kan satar kayan abincin 1,000
- Jirgin Flynas zai kwaso rukunin farko na Alhazan Nijeriya
Da yake tsokaci game da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, mai magana da yawun gwamnan ya ce abin da Sarkin ke yi bai yi kama da halayyarsa ba.
Ya ce “Amimu Bayero ɗan asalin Kano ne, ana girmama shi kuma ba ma so wani abu ya same shi. Babu wanda ya takura masa kan cewar ya bar jihar. A matsayinsa na mutum mai daraja yana da damar tafiyar duk inda yake so.
“’Yan sanda sun ɗauki ɓangare a yanzu, ba sa karɓar umarni daga wajen gwamna.
“Tun da Aminu ya iso cikin dare lokacin da shi da iyalinsa suka bar babbar fada, sun ɗebe kayansu daga fada amma wasu ‘yan siyasa masara kishi sun dawo da shi domin tayar da tarzoma.
“A wajenmu faɗa ne da za a ƙarasa domin gwamna yana da iko da damar cire ko naɗa sabon Sarki. Kundin tsarin mulki ya ba shi dama kuma babu wanda ya isa ya ƙwace masa. Ko da za a ɗauki shekara 100 gwamna yana da wannan ‘yancin ya cire ko naɗa Sarki.”
Aminiya ta ruwaito cewar dambaruwar masarautar Kano na ci gaba da jan hankali a jihar, inda lamarin ke ci gaba da haifar da ruɗani da cece-kuce a tsakanin al’ummar jihar.