✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano: Gwamna Abba ya nada sabon Akanta-Janar

Abdulkadir Abdussalam ya zama sabon Akanta-Janar na Jihar Kano, Garba Ahmed Bichi kuma ya zama Manajan Daraktan Hukumar Ruwa

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya nada sabon Akanta-Janar na jihar da wasu sabbin mukamai a gwamnatinsa.

Sanarwar da Babban Sakataren Watsa labaran gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu, ta ce gwamnan ya nada Abdulkadir Abdussalam a matsayin Akanta-Janar na Jihar Kano.

Injiniya Garba Ahmed Bichi kuma ya zama Manajan Daraktan Hukumar Ruwa ta Jihar Kano, sai Dokta Rahila Mukhtar a matsayin Babbar Sakataren Hukumar Kula da Gudunmawar Kiwon Lafiya ta Jihar Kano (KCHMA).

Haka kuma an nada Hassan Baba Danbaffa a matsayin Manajan Darakta na Hukumar Kula da Tituna ta Jihar Kano (KARMA), da Arc. Ibrahim Yakubua matsayin Manajan Daraktan Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano (KNUPDA).

A cewar sanarwar nan ba da jimawa ba za a sanar da lokacin rantsar da wadanda aka nada domin ba su damar sauke nauyin da aka dora musu nan take.