Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kafa wani kwamitin da zai binciki zargin karkatar da Naira miliyan 352 a Jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil a jihar.
A kwanakin baya ne wani kwamiti da aka kafa don binciken mahukuntan jami’ar kan zarge-zarge ya mika rahotonsa ga gwamnati.
- Ban gamsu da sakamakon zaben Kenya ba, an tafka magudi — Raila Odinga
- Mutumin da ya yanke gabansa yana tsaka da mafarkin yanka nama
Daga cikin shawarwarin da kwamitin ya bayar kuma har da na bukatar bincikar yadda ake zargin karkatar da kudaden, wadanda aka ce na fanshon ma’aikatan jami’ar ne.
Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da kafa kwamitin a cikin wata sanarwa ranar Talata.
Ya ce Gwamna Ganduje ne ya kafa kwamitin wanda ya kunshi hukumomin gwamnati da dama domin bin diddigin zarge-zargen.
A cewar Kwamishinan, kwamitin zai kasance karkashin Manyan Sakatarori na Ofishin Shugaban Ma’aikata na Jihar da Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar da na Asusun ’Yan Fansho da na Ma’aikatar Kudi da Babban Mai Bincike na jihar.
Sauran sun hada Mai Bincike na Kananan Da Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta jihar da Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi wadanda dukkansu za su kasance mambobin kwamitin.
Bugu da kari, sanarwar ta ce Babban Sakataren Ma’aikatar Shari’a na jihar ne zai kasance Sakataren kwamitin.
Kwamishinan ya kuma ce nan ba da jimawa ba Gwamnan zai rantsar da kwamitin a wata ranar da za a sanar a nan gaba.