A yau ne daliban aji daya (JSS1) na karamar sakanda da babbar sakandare (SS1) suka koma makaranta a jihar Kano.
Kwamishinan Iliminjihar, Muhammad Sanusi Kiru, ya sanar da hakan a sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na ma’aikatar Aliyu Yusuf fitar.
- Hotunan yadda dalibai suka koma karatu a Kaduna da Kano
- Yadda ’yan kwana-kwana suka ceto mutum 132 a Kano
- ’Yan aji dayan sakandare a Kano za su koma makaranta ran Litinin
- ‘Ciyar da daliban Kano kan lakume N4bn duk shekara’
“Ya kamata daliban makarantun Firamare 1-6 su sake komawa gaba daya daga ranar Litinin, 16 ga Nuwamba, sabanin umarnin farko da aka sanya musu ranakun zuwa makaranta”, inji shi.
Ya yi kira ga iyayen da yaransu ke wadannan azuzuwan da su yi biyayya ta hanyar dawo da su a ranakun da aka sanya.
Daga nan sai kwamishinan ya umarci daraktoci da shugabannin makarantu da sauran masu ruwa da tsaki da su kasance cikin shiri don ci gaba da aikin.
Idan ba a manta ba, gwamnatin jihar ta umurci daliban JSS-1 da SS-1 da su kasance a gida na tsawon makonni biyar domin an kammala jarabawar masu kammala karama da babbar sakandare.