✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kano: APC ta buƙaci jami’an tsaro su kama Kwankwaso

APC ta ce akwai buƙatar jami'an tsaro su tuhumi Kwankwaso game da kalamansa.

Jam’iyyar APC a Jihar Kano ta bayyana kalaman da jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi a matsayin abun takaici.

Jam’iyyar ta maka Kwankwaso a kotu domin a kama shi bisa zargin da ya yi na cewar gwamnatin tarayya na yin katsa-landan cikin harkokin Kano.

Shugaban jam’iyyar na jihar, Abdullahi Abbas, cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce babu wata barazana da Kwankwaso zai iya yi wa gwamnatin tarayya.

Aminiya ta ruwaito yadda Kwankwaso ya yi zargin gwamnatin tarayya ƙarkashin jam’iyyar APC na yunƙurin kawo cikas ga zaman lafiya a jihar.

Kwankwaso, ya bayyana haka ne a lokacin bikin ƙaddamar da aikin titi mai tsawon kilomita 85 a mahaifarsa ta  Madobi da gwamnatin jihar ta yi.

“Jigon jam’iyyar NNPP, wanda a bayyane yake cewar yana cikin damuwa saboda gaza taɓuka abun a zo a gani da jami’yyarsa ta yi cikin shekara guda, kuma yana da burin ganin ya mallaki siyasar Kano, ya kamata jami’an tsaro su kama shi domin ya shaida waɗanda suke horar da ‘yan Boko Haram.

“Muna kira ga jami’an tsaro da kakkausar murya da su kamo wannan mutum domin ya bayyana sunayen waɗanda ya kira maƙiyan jihar da ke yi wa gwamnatin tarayya aiki domin horar da ’yan Boko Haram da masu tayar da ƙayar baya.”

Idan ba a manta ba dai, Kano na cikin ruɗani kan rikicin masarautun jihar, inda a yanzu haka sarakuna biyu ke mulki.

Muhammadu Sanusi II na mulki daga babbar fadar masarautar Kano da ke gidan Rumfa, yayin da Aminu Ado Bayero ke mulki daga fadar Nassarawa a jihar.