✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kano 2023: Dalilin ba wa Gawuna takarar Gwamna —Ganduje

Biyayya ta sa muka tsayar da Gawuna takarar Gwamnan Kano, in ji Ganduje.

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce kwarewar mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna, ce ta sa masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC a jihar suka tsayar da shi takarar gwamna a zaben 2023.

Da yake jawabi a wajen taron gidauniyar da abokin Gawuna ya shirya a Abuja,Ganduje a ce babu wata jam’iyya a Kano da ke da dan takara kwararre irin mataimakin nasa.

“Dokta Gawuna na sane da shirye-shirye da kuma ayyukanmu, kuma mun yi amannar mutum ne wanda zai taimaka wa cigaban al’umma.

“Wannan shi ne irin mutanen da muke raino, wadanda za su yi tsayin daka wajen ci gaba daga inda aka tsaya da kyawawan ayyukan bunkasa al’umma da aka asassa. In sha’a Allah za mu ci gaba da haka,” in ji gwamnan.

Gwamnan ya ce, da ilimi da kwarewa da kuma kyakkyawar mu’amalar Gawuna da jama’a ne suka karfafa zaben nasa.

A cewarsa, “Daya daga cikin abubuwan da muka yi la’akri da su shi ne ci gaba da ayyuka saboda muhimmancin hakan a sha’anin shugabannci.

“Mun tattara bayanan cigaban da muke bukata, kuma muddin aka rasa ci gaba wajen aiwatarwa abubuwa za su watse, ba za mu kai ko’ina ba.”

Gwamnan ya ambato lokacin da yake mataimaki a gwamnatin Kwankwaso inda suka yi aiki tare don cigaban Jihar Kano.

“Shi ya sa bayan ya tafi ban bukaci sai wani ya fada mini ayyukan da zan aiwatar ba saboda na san komai, kuma ba ni da dalilin yin watsi da su,” in ji shi.

A nasa bangaren, Gawuna ya ce ci gaba daga inda gwamnatin baya ta tsaya shi ne sirrin samun kyakkywan sakamako.

Ya kara da cewa, “Kwarewata na da muhimmanci, kuma a shirye nake in yi amfani da ilimin da na koya na shekaru wajen yi wa jiharmu hidima.”