Kwamitin karbar mulki na Gwamnan Kano mai jiran gado Injiniya Abba Kabir Yusuf ya zargi Gwamna Abdullahi Ganduje da yi wa shirinsu kafar ungulu don ganin ba a karbi mulki lafiya ba.
Shugaban Kwamitin, Dokta Abdullahi Baffa Bichi ya ce duk da cewa gwamnati mai barin gado ta kafa kwamitin bayar da mulki mai membobi 17, amma har yanzu ba ta kaddanar da kwamitin ba ballantana ya fara gudanar da ayyukansu
- Kalli Yadda Aka Yi Bikin Nadin Sarauta A Fadar Sarkin Kano
- An kashe hatsabibin dan ta’adda ya je garkuwa da dan kasuwa a Katsina
Baffa Bichi ya shaida wa taron maneman labarai a Kano cewa kwamitinsa na zargin jan kafar gwamantin a matsayin yankan baya ga gwamnati mai shigowa..
Ya kuma koka game da manufar da gwamnati mai ci ke da ita wajen yin kwamiti guda daya don gudanar da shirin bayar da mulki.
“Mun fahimci ita gwamnati mai ci tana kokarin ne mu hada kwamiti guda daya da su inda ta nemi mu bayar da mutane 3 ita kuma ta bayar da mutane 17 wanda kuma hakan ba mai yiyuwa ba ne domin jamiyyyu ne biyu masu manufofi daban-daban don haka dole a yi kwamitoci guda biyu don yin aiki tare. Wannan ba sabon abu ba ne,” in ji shi.
Kwamitin ya bayyana cewa tunda Gwamnatin Ganduje ta ki yarda a zauna da jami’anta kwamitin ba shi da zabi illa ya gayyaci manyan ma’aikatan gwamnati don tattaunawa da su a kan ayyukan ma’aikatunsu.
“Za mu fara zaman tattaunawa da manyan sakatarorin ma’aikatu daban-daban a ranar 2 ga watan Mayu. Sannan za mu zauna da manyan daraktocin hukumomin gwamnati da kuma shugabannin ma’aikatan na kananan hukumomi 44 wanda za mu yi a wasu ranakun daban-daban.”
Kwamitin ya yi kira ga Gwamna Ganduje da ya gaggauta yin abin da ya kamata wajen ganin ya bayar da hadin kai ga Jam’iyyar NNPP don karbar mulki cikin nasara.
In ji shi, “Muna kira ga Gwamna Ganduje da ya farka daga magagin da ya same shi, ya kuma yarda da kaddara cewa Abba ya zama Gwamnan Kano don haka ya bari a gudanar da bayar da kuma karbar mulki lami lafiya ba tare da fitina ba.”
Kwamitin ya tabbatar wa jama’ar Jihar Kano cewa zai jajirce wajen ganin an gudanar da shirye-shiryen karbar mulki lafiya wanda zai bayar da dama ga sabuwar gwamnati ta yi musu ayyukan da suke burin ta yi musu.
Yayin da yake mayar da martani, Kwamishinan Wattsa Labarai na Jihar Kano kuma mamba a Kwamitin Bayar da Mulki da gwamnatin jihar ta kafa, Muhammad Garba ya bayyana cewa babu gaskiya a cikin dukkanin zarge0zargen da kwamitin ya yi.
Muhammad Garba ya ce Kwamitin na Jam’iyyar NNPP ne ma ya ki bayar da mutanensa guda uku kamar yadda suka nema.
“Abin da ya sa muka nemi su ba mu mutum uku wadanda za su yi aiki tare da namu mutane 17 din saboda yawancin aikin da za a yi yana wuyan gwamnati mai barin gado ne.”
Muhammad Garba ya karyata batun cewa kwamitin nasu ba ya aiki saboda wai Gwamna Ganduje bai kaddanar da su ba, inda ya ce akalla kwamitin ya zauna sau biyu inda shugaban kwamitin ya umarci ma’aikatu da sauran hukumomin gwamnati da su ci gaba da aikin mika mulkin.
“Tuni wadansu daga cikin ma’aikatun suka kammala aikin mika bayanan da suka shafi maaikatunsu.
“Abin da muke jira shi ne su ba mu membobin da za su wakilce su don ci gaba da aikin bayarwa tare da karbar mulkin”