✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kannywood: Muhimman abubuwa 5 da suka faru a makon jiya

Daso ta bude wurin taron biki wato Event Center.

Akwai wasu muhimman abubuwa da suka faru cikin makon jiya a masana’antar wasan kwaikwayo ta Kannywood da Aminiya ta rairayo wasu daga cikinsu domin nishadantar da masu karatu.

Ga wasu daga cikinsu kamar haka:

Fim din Sarki goma zamani goma ya hada kudi Naira 3,707,500

Fim din Sarki goma zamani goma ya tara kudi Naira dubu 335,500 a karshen makonsa na hudu sinima.

Yanzu fim din wanda Abubakar Bashir Maishadda ya shirya kuma Ali Nuhu ya ba da umarni, ya hada kudi jimilla Naira 3,707,500.

A cikin fim fim akwai jarumai irinsu Mommee Gombe da Aisha Izzar So da Rayya Kwana 90 da Maryam Yahaya da Amal Umar da Umar M. Shareef da Shamsu Dan Iya da sauransu.

Kannywood ta tuna da Isiyaku Forest

Masana’antar Kannywood ta tuno da marigayi Isiyaku Forest.

Marigayi Isiyaku Forest yake gaisawa da Shugaba Buhari a tare da shi akwai Baban Chinedu da MC Tagwaye da Malam Ibrahim Yala

Malam Ibrahim Yala ne ya sanya hoton marigayin tare da Shugaba Buhari, sannan ya yi masa addu’ar samun rahama a wajen Allah.

Adam A. Zango akwai biyayya ga uwa — Jamilu Kochila

Adam A. Zango tare da mahaifiyarsa Furera da jaririyarsa Diyana

Jamilu Kochila ya bayyana cewa jarumi Adam A. Zango yana da kokari wajen biyayya da kula da mahaifiyarsa.
A cewar shi, “in dai biyayya ga uwa da kyautata mata ne, ka dace. Ni shaida ne abokina. Ni shaida ne. Allah Ya raba ku lafiya.”

A makon jiya ne aka yi sunan diyar jarumin wanda shi da kansa ya tabbatar da cewa ya sanya wa ’yarsa sunan mahaifiyarsa.

Wani sako da Jarumin ya wallafa a shafinsa na Instagram ya ce, “Godiya ta tabbata ga Allah S.W.T! Allah Ya raya mana ita bisa turbar addinin Musulunci.

“Allah Ya shirye ta Ya sa Annabi Muhammad S.A.W ya yi alfahari da ita ranar lahira! Sunanta Furaira Adam. Sunan mahaifiyata ne. Amma sunan kunyarta Princess Diyanah.

Saratu Gidado ta bude wajen taro

Jaruma Saratu Gidado, wadda aka fi sani da Daso ta bude wurin taron biki wato Event Center.

Ta sanya wa wajen bikin Daso Event Center domin biki ko suna ko kamu da sauransu.

An bude wannan waje a birnin Dabo wato Jihar Kano.

Kofar shiga Daso Event Center

Wani bidiyo da Aminiya ta gani ya nuna yadda Daso ta yi wani dan kwarkwaryar biki na bude wurin taron, inda ta yanka igiyar bude sabon wurin tare da rakiyar wasu daga cikin tsofaffin jaruman masana’antar irinsu Rukayya Dawayya da sauransu.

Haka kuma akwai Nura M. Inuwa da Dauda Kahutu Rarara da suka halarci bikin.

Daso ta ce za su dauki ma’aikata akalla 100 a wajen.

Shin ko Rahama Sadau ta dawo Kannywood?

Rahama Sadau tana Jihar Adamawa a yanzu haka inda ake daukar wani fim mai suna Gambo da Sambo wanda take ciki.

A cikin jaruman fim din akwai Rahama Sadau da Sani Danja da Magaji Mijinyawa da Daushe da sauransu.

Rahama Sadau da Sani Danja a wajen daukar shirin

Sai dai fim ne na Furodusa kuma Darakta a Nollywood wato Dambo Atiya, wanda ya shirya fim din Sons of the caliphate. Ke nan mashiryin fim din dan Kudu ya zo domin shirya fim din a Arewa. Fim din barkwanci ne.