✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kani ga tsohon Gwamnan Kano, Kwankwaso, ya rasu

Ya rasu yana da shekara 64 bayan fama da gajeruwar jinya.

Kani ga tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wato Kwamared Inuwa Musa, ya rasu.

Sanarwar rasuwar tasa na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Yada Labarai na Kwankwasiyya, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Litinin.

A cewar sanarwar, “Cikin mika lamuranmu ga Allah, muna sanar da rasuwar Kwamared Inuwa Kwankwaso, kani ga tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.”

Ya rasu yana da shekara 64 da sanyin safiyar Litinin, 20 ga watan Disamban 2021, a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke Kano, bayan wata gajeruwar jinya.

Marigayin dai tsohon ma’aikacin gwamnati ne da ya yi ritaya a matsayin Injiniyan Gona, kuma ya yi karatu a birnin Ibadan na Jihar Oyo da kuma kasar Amurka.

Ya kuma shafe tsawon shekaru yana aiki a matsayin jami’in dashen bishiyoyi a Jihar Kano.

Ya rasu ya bar mace daya da ’ya’ya biyu – Barista Nafisa Inuwa da Zainab Inuwa – da kuma ’yan uwa da dama.

Tuni dai aka ji jana’izarsa a garin Kwankwaso da ke Karamar Hukumar Madobi a Jihar Kano, kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.