✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kanawan da suka kafa gari a kasar Indiya

“Indiya ga rawa ga waka,” a wani kirari da Hausawa ke yi wa mutanen kasar da aka yi sabo da su ta hanyar fin-finansu. Sai…

“Indiya ga rawa ga waka,” a wani kirari da Hausawa ke yi wa mutanen kasar da aka yi sabo da su ta hanyar fin-finansu.

Sai dai ba kamar yadda muka saba ganin su a fina finai farare ba, a kasar Indiya da akwai bakaken fata a kasar mai al’ummu daban-daban da yawansu ya haura miliyan 100.

Cikinsu kuwa har da wadanda aka ce sun yi ikirarin asalinsu daga Kanonmu ta Dabo.

Wadannan Indiyawa bakaken fata su ne ‘shimali Indiya’ a cewar wani rahoton Premier Radio wanda ta wallafa a shafinta na dandalin sada zumunta ya kuma karade intanet.

Rahoton ya ce wadannan Indiyawa na zaune ne a jihar Gujurati da kuma sun yi fice a sarrafa duwatsu masu daraja domin yin abin wuya da sauran kayan ado na mata.

Indiyawan-Kanawa sun ce Kakanninsu ne suka yi kaura na fatauci sama da shekaru 500 da ya wuce daga birnin na Dabo zuwa kasar Indiya a inda suka tare da kwarewa a sarrafa duwatsu masu daraja da ake shirya kayan adon mata na Tsakiya da Jigida da sauransu.

Sun kuma yi hijarar ce a shekarun masu yawa da suka wuce karkashin shugabansu mai suna Baba Gori, in ji rahotan.

Indiyawan musu ikirarin Kano a yanzu suna zaune a garuruwan Barrat da Ratampur da kuma Jumakumput duk a cikin Jihar ta Gujurat, suna kuma rike da addinsu na Musulinci sai dai al’adar Hausawa da kuma yaren na Hausa ya bata domin sun koma Indiyawa sak, a cewar rahoton.

Shaharar malam Bahaushe na hada-hadar kasuwanci ya shahara a duniya inda ta kai wasu Hausawa suka watsu a duniya domin neman na halak wanda hakan ta sa ake samun matsugunin Hausawa a kasashen duniya na kusa kamar Ghana da Gabon da Kongo da saura kasashe nahiyar Afrika da na larabawa da wasu kasashe daban-daban na duniya.

Wannan rahato da ya ja hankalin jama’a ya dada tabbatar da kirarin da ake yi wa Bahaushe na “dan Duma mai kai ’ya’yanta nesa,” in ji masu karin magana.