A jihar Kano, daya daga manyan cibiyoyin kasuwanci a Najeriya, mazauna na kokawa kan yawan ayyukan gyaran hanya da aka fara amma daga baya aka yi watsi da su.
A lokacin rani hanyoyin kan tirnikewa da kura da ke kawo barazana ta lafiya musamman ga masu cutar asma da makamantanta.
Da damina kuwa yawan ruwan da kan malale hanyoyin hadi da wanda yake kwanciya a cikin ramuka kan jawo matsaloli da dama.
Ta bangaren kasuwanci kuwa, masu shagunan da ke makwabtaka da irin wadannan hanyoyi na kokawa cewa lamarin ya yi sanadiyyar raguwar cinikin da suke samu saboda jama’a na kaurace wa hanyoyin.
Masu sayayya kan guje wa irin wadannan shagunan saboda kurar da ke tashi a kan hanyoyin da ke kusa da su.
Mazauna yankunan da abin ya shafa sun ce yawancin ayyukan gwamnatocin baya ne suka faro su, amma daga baya magadansu suka yi watsi da su.
Titin Inuwa Dutse
Titin Inuwa Dutse, hanyar da ta hada unguwannin Darmanawa, Karkasara (bayan Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano), Sallari da kuma titin Court Road, an yi watsi da hanyar tsawon shekaru. Saboda haka ake yawan samun tashin kura da ke damun mazauna da kuma masu bin hanyar.
Hanyar, a ta bakin wani mai shago ta shafe shekaru a haka, kuma ba su san takamaiman lokacin da aikinta zai ci gaba ba.
Saleh Abdullahi wanda yake da shagon sayar da lemon kwalba da ruwa ya ce ba zai iya tuna shekarar da aka fara aikin da farko ba kafin daga bisani a yi watsi da shi.
Ya ce, “Saboda mawuyacin halin da hanyar ke ciki, cinikinmu ya ja baya matuka saboda babu wanda yake son bin hanyar.
“Wasu lokutan za ka saro lemo amma bayan kamar kwanaki biyu ko uku sai ka ji masu saye suna korafin wai ko wanda ya lalace kake sayar musu saboda kurar da take bade su.
“Saboda haka mutane da yawa kan gwammace su tafi wasu wuraren don yin sayayyar”, inji Saleh.
Aminiya ta lura cewa ramukan da ke kan hanyar sun tilasta wa masu ababen hawa komawa amfani da hannu daya.
Hakan inji Abdullahi ya kara yawan hatsarin da ake yi a kan hanyar cikin ‘yan watannin nan.
Tsaka mai wuya
A kusan dukkan hanyoyin, lamarin na da matukar wuyan sha’ani ga mazauna da kuma masu amfani da hanyoyin.
A cewar Abdullahi na Karkasara, lokacin da kawai suke samun sa’ida daga kurar hanyar shi ne idan an yi ruwan sama.
“Idan kuma aka yi ruwan saman, sai ramukan hanyar su cika da ruwa, wani wurin ma ya ki biyuwa, to ka ga ala ayyi-halin dai lamarin ba sauki.
“Shaguna 20 ne suka yi kaura saboda rashin kyan hanya”, inji shi.
Titin Yahaya Gusau
A kan titin Yahaya Gusau wanda ya hada rukunin masana’antu na Sharada da Gadon Kaya, kimanin shago 20 ne suka yi kaura daga wani gida saboda rashin kyan hanyar.
Da yake tabbatar da lamarin, wani mai shagon sayar da kayan babura a kan titin, Muhammad Baba, ya ce, “Ka ga wancan gidan (ya nuna wani bene), kimanin shaguna 20 da aka kama haya, amma yanzu duk sun tashi saboda matsalar hanyar.
“Idan ka kasa kaya, kura ce za ta lullube su, kuma ka san abin da hakan ke nufi (ba wanda zai saya).
An shafe shekaru ana aikin
“Wannan hanyar da ba ta wuce kilomita biyar zuwa bakwai ba ta haura shekaru bakwai ana aikinta, ko da yake na ga wasu ‘yan tsirarun motoci sun dawo aiki a kanta makon da ya wuce.
“Duk lokacin da aka yi ruwa hanyar ba ta biyuwa ballantana ma a yi maganar yin ciniki, ko ka bude shagon ma sai dai ka zauna ku yi ta hira”, a cewarsa.
Aminiya ta lura cewa ya kamata zuwa yanzu a ce an karbi hayar kantunan da aka gina a kan hanyar zuwa, amma kuma babu kowa a cikinsu.
‘Yan kalilan din da aka kama kuma masusu na korafin rashin samun ciniki.
“A lokacin da aka fara aikin a baya sai da aka kusa kammalawa kafin a yi watsi da shi daga bisani.
“Yanzu da aka dawo ka ga sai an sake kusan tun daga farko saboda duk ruwa ya zaizaye cikon da aka yi.
“Hakan na sa gwamanti ta kara yin asarar kudadenta kenan. Aikin da ya kamata a kammala a Naira 70 alal misali, sai ka ga ya lakume Naira 120 ko ma 150 sakamakon kin kammalawa a kan kari”, inji Baba.
Unguwar Dandinshe
A unguwar Dandinshe ma ba ta sauya zane ba. Hanyar na da matukar muhimmanci kasancewar ite ce ta hada yankin da Kofar Dawanau take kuma sada su da sauran sassan birnin Kano.
Anguwar wacce ke karamar hukumar Dala, bincike ya nuna ita ce mazabar siyasa ta biyu mafi girma a Najeriya saboda yawan al’ummarta.
Amma duk da muhimmancinta a siyasance, al’ummarta na kokawa game da shakulantin-bangaro da gwamnatoci da dama suka yi da su.
Wani mazaunin yankin ya ce watsi da aikin hanyar ya shafi rayuwarsu ta bangarori da dama.
Mazauna na wahala
Malam Balarabe Shehu mazaunin yankin ne, ya ce, “Mata masu juna biyu da yawa sun haihu kan hanyar zuwa asibiti saboda ramukan kan hanyar nan.
“Duk wanda yake a wannan unguwar zai yarda da ni cewa hatta farashin abin hawa da muke biya ya sha bamban da na sauran unguwanni saboda rashin kyan hanya.
“Dandinshe unguwa ce mai dimbin jama’a, amma lokacin da kawai suke waiwayar mu shi ne lokacin yakin neman zabe.
“Kusan duk ‘yan siyasa da ita suke mana alkawari, amma da zarar mun zabe su shi ke nan sai lamarin ya zama tarihi”, inji shi.
‘Da gangar aka yi watsi da aikin’
Shi kuwa wani mazaunin unguwar da aka sakaya sunansa na zargin cewa da gangan gwamnati mai ci ta yi watsi da aikin hanyar don kawai magabaciyarta ce ta fara shi.
“Kafin zaben 2019, aiki ya dawo a kan wannan hanyar kamar da gaske, kawai sai tsautsayi wata rana gwamna ya zo wucewa aka yi masa ihu, sauran kuma sai tarihi”, inji shi.
‘Gwamma jiya da yau’
Titin New Road da ke unguwar Sabon Gari a Karamar Hukumar Fagge na daya daga cikin irin wadannan titunan da aka yi watsi da aikin gyaransu.
Wata mazauniya kuma mai shago a titin, Misis Edna Ibe ta shaida wa Aminiya cewa an barje hanyar amma daga bisani aka yi watsi da ita yau kimanin shekara bakwai ke nan.
“Kwanan nan wani nakasashshe ya fada cikin wannan kwatar (ta nuna wani katon rami), sai da na zub da hawaye don tsabar tausayi. Kullum sai ka ji masu ababen hawa suna Allah-wadai saboda munin hanyar nan”, inji Misis Edna Ibe.
Kamar a titin Yahaya Gusau, mazauna titin na New road da dama sun ce sun gwammace da an bar musu hanyar yadda take a da can.
A ina gizo ke saka?
Rashin ci gaba da ayyukan da gwamnatoci suka gada ita ce babbar matsalar ta hanyoyin na Kano, inji mazauna yankunan.
Titin Dakata zuwa Bela alal misali shi ma yana cikin wannan matsalar domin aikin gyaransa ya tsaya ne a iya Kwanar Inusawa. Haka abin yake a titin Rimin Kebe, dukkanninsu a Karamar Hukumar Ungogo.
Mazauna titin Shaikh Mahmud Salga da ya tashi daga Jakara zuwa Goron Dutse su ma sun dade suna rokon gwamnati ta karasa aikin.
Hanyar na da matukar muhimmanci saboda ita ke sada wasu sassan birnin Kano da kasuwar Kurmi mai dadadden tarihi.
‘Yan kasuwar sun koka kan cewar yanzu ba su samun ciniki kamar a baya musamman daga jihohin Sokoto da Zamfara saboda rashin hanyar.
‘Aiki na ci gaba, bai tsaya ba’
To sai dai da yake mayar da martani, Babban Sakataren Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar Kano, Ahmed Abba Salisu ya ce ba gaskiya ba ne a ce gwamna Ganduje ya ki karasa ayyukan da ya gada daga gwamnatocin baya.
Ma’aikatar ta kasance babu kwamishina tun da aka dakatar da Injiniya Mu’az Magaji daga jagorancinta.
Babban sakataren ya ce gwamnatin ta kammala ayyukan gwamnatocin da ta gada a baya da yawa, yana mai bayar da misali da asibitin yara na Isyaka Rabi’u da ke titin Zoo Road da kuma aikin gadar sama ta Sabon Gari mai tsawon kilomita biyu.
Salisu ya ta’allaka tsaikon da aka samu a wasu ayyukan kan annobar COVID-19, ko da yake ya ce yanzu abubuwa sun fara dawowa.
Ya bayar da misali da titin Yahaya Gusau da ya ce yanzu haka aikin ya dawo.
Jami’in ya kuma ce tuni gwamnati ta umarci a dawo da ayyukan titunan masu tsawon kilomita biyar-biyar a kowacce karamar hukumar da ke jihar wadanda a baya suke karkashin Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano (KNUPDA) zuwa ma’aikatar tasu domin kammalawa.
Ya ce anyi hakan ne don tabbatar da an karasa ayyukan gaba daya.
Ya yi kira ga al’ummar yankunan da lamarin ya shafa da su kara hakuri, yana mai cewa gwamnatin na da zummar kammala dukkan ayyukan da ma wasu a nan gaba.