✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘kananan masana’antu ne tushen bunkasar tattalin arzikin kasa’

Shugaban Kamfanin Samar da Ruwan Leda na IMG wato Pure Water, Alhaji Idris Musa Garki ya bayyana cewa kafa kananan masana’antu zai kara bude hanyoyin…

Shugaban Kamfanin Samar da Ruwan Leda na IMG wato Pure Water, Alhaji Idris Musa Garki ya bayyana cewa kafa kananan masana’antu zai kara bude hanyoyin samun ayyukan yi ga al’umma tare da bunkasa tattalin arzikin ba tare da dogara da samun aikin gwamnati ba.
Ya yi wannan bayani ne cikin wata zantawa da ya yi da Aminiya, inda ya nuna cewa “kananan masana’antu su ne tushe na farko wajen inganta dogaro da kai da kuma bude hanyoyi na gyaran tattalin arziki musamman ganin cewa  lokaci ya yi na  kara yawansu a birane da kuma yan kunan karkara.”
Har ila yau, ya sanar ya bayyana cewa kasashen da suka ci gaba ta fuskar masana’antu sai da suka fara kakkafa kananan masana’antu kafin sannu a hankali suka fara samar da matsakaitan kamfanoni har zuwa manya wajen sarrafa abubuwan da suke samarwa zuwa kasashen duniya.
Alhaji Idris ya kara da cewa Allah Ya bai wa  kasar nan dimbin albarkatun kasa wadanda ake bukata  domin sarrafawa a kowane kamfani, don haka a cewarsa lokaci ya yi da masu hannu da shuni za su kara kakkafa kananan masana’antu ta yadda  Najeriya za ta bi sahun sauran kasashe masu karfin tattalin arziki na masana’antu da kuma samar da ayyukan yi  ga al’umma.
Ya ba da misali da yadda kamfaninsa na samar da ruwan leda da ke unguwar Dawanau ya samar da ayyukan yi ga mutane fiye da 25 tare da bunkasa dogaro da kai ga al’umma musamman ganin “cewa lokaci ya yi da za a kara yawan kananan masana’antu a Jihar Kano da kuma kasa baki daya ta yadda za a hada hannu wajen kyautata zamantakewar  al’umma da farfado da darajar tattalin arzikin kasa ta fannin kasuwanci.
Har ila yau, ya bukaci gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da su kara samo hanyoyin inganta samar da wutar lantarki wadatacciya domin a cewarsa, kamfanoni suna bukatar isashshiyar wutar lantarki muddin dai ana so su  ci gaba da aiki kamar yadda abin yake a zamanin baya.
Daga nan ya bayyana cewa  kafa masana’anta yana da  sharudda da kuma ka’idoji daga hukumomin gwamnati domin tabbatar da ganin cewa komai yana bisa doka, don haka ya ce yana da kyau masu aniyyar kafa kamfanoni su yi la’akari da haka tare da yin hakuri kafin komai ya zamo cikin nasara   da  kuma  nagarta.
A karshe ya jaddada da cewa kamfaninsa zai ci gaba da bullo da karin hanyoyi na ba da guraben ayyukanyi, musamman ganin yadda ma’aikatansa suke kokari wajen rike gaskiya da tabbatar da tsaftar masana’anta a kodayaushe.