Kamila, sabon wake ne da Dokta Aliyu Tilde ya rubuta, inda yake ba Shugaban kasa Mai Jiran Gado, Muhammadu Buhari shawara, musamman game da halaye goma na shugaban kirki da kuma munanan dabi’un mabiya. Mu nazarci waken cikin natsuwa, domin fa’idantuwa da darussansa:
Mutafaa’ilun Mutafaa’ilun
Bahari na Kamilu ya tsaya.
Duka godiya haka nan yabo
Duka naka ne haka gaskiya.
Matsayinmu wanda muke ciki
Sha’aninKa ne Mara-kishiya.
Tsanani cikin lamura duka
Ka kawar da shi duka bai daya.
Duka zalumi ka kifar da shi
Da ganinsa sai a yi dariya.
Fatara ta zo masa nan da nan
Ya yi zamani a cikin tsiya.
Rikici ka sa ya nutsar da shi
Haɗari ya kai masa har wuya.
Shagali ko har bidiri daɗa
Abadan su zam duka sai jiya.
Matsayi kuma ya zame ahir
Ya zamo rabo duka ba shiya.
Ka daɗa masa matsala yana
Mutuwa cikin tsananin wuya.
Lamarin ƙasa ka saka hanun
Wani kamili mara murdiya.
Ka taya masa a dukan waje
Ya zame kamar fitila daya.
Wace za mu bi a cikin ladab
Haka har ya zam mana kariya.
Ya riƙe mu har ya zame mana
Mariƙi ya zam mara wariya.
Dukanin ƙasa ta zame guda
Rukuna su zam duka lafiya.
Masana suna iya shawara
Ta zamo abin a yi fariya.
Duka ’yan ƙasa su tsayin daka
Su yi ƙoƙarin su yi gaskiya.
Da biɗar halal duka lokaci
Da wada a kowace rariya.
Haka in akwai wasu cutuka
A kawar a zam duka lafiya.
Tafiya idan ta taho a yi
A cikin shiri haka lafiya.
Duka shugaba a tarar da shi
A cikin su goma da ba wuya.
Ka matso ina maka zayyana
Wada za ka sansu gaba ɗaya.
Ya zame da son ya yi gaskiya
kudiri guda daga zuciya.
A ganai a ce masa adali
Duka nasa ne mara wariya.
Kada ɗai ya zam mutajabbiri
Da yake da son ya yi danniya.
Ilimi ya zam fitila garai
Da sani yake tafe duniya.
Na biyar ya zam ya yi shawara
Lamari ya zam bisa gaskiya.
Haka nan ya ɗau haƙuri da mu
Mabiya yana mana tausaya.
Na bakwai ya zam kuma jarumi
Ya tsayin daka bisa gaskiya.
Da gudun abin duka duniya
Zuhudun ya zam masa kariya.
Ya sani rabonsa yana jira
A wajen Karimu gaba ɗaya.
Na tara: Aro aka ba shi yau
Wa’adi yana tafe, ka jiya?
Daɗa shekara huɗu ba wuya
Da takwas kamar a yi walƙiya.
Haka kar ya ɗau wasu ayyuka
Ya saka hanun mara gaskiya.
Daga nan wajen muyi ta-natsu
Talaka mu tanadi gaskiya.
Matsala mu san duka mu muke
Daɗa ƙarfafa ta a duniya.
Kwaɗayi da son a yi fankama
Biyu sun kashe mana zuciya.
Da rashin mu nemi na kai daɗa
Suka sa mu dau mara gaskiya.
Daga ya aje mana ’yan kuɗi
Mu cene ba ai ba kamar shiya.
Sha’awa ya sam mana ko kaɗan
Mu cafe mu zam masa godiya.
Daga mai dubu, miliyon gama
Duka ba mu yin wata tambaya.
Da irin zaton da muke da shi
Matsalarmu san da muke wuya.
Duka gwamnati muka sa ido
Ta kawar da shi a bugu daya.
Akasin hakan mu yi tsinuwa
Daga nan mu ce masa ɗan tsiya.
Da ƙashin tsiya a gare shi ai
Haka nan muke ta ashariya.
Bara ma ya zam kuma takara
Da ƙwafa mu zam masa dariya.
Mu sani hakin ita gwamnati
Abu ne guda bisa gaskiya.
Yanayin ƙasa haka kasuwa
Su zame da kyau mara sa wuya.
Duka ɗan ƙasa ya yi walwala
A biɗar halal mu zame ɗaya.
Yanayin da ba wani fargaba
Mu bi ƙa’ida mu bi gaskiya.
Haka gwamnati ta yi tattali
Da barin yawan bidirin tsiya.
Daga gwamna ko kuma shugaba
Suka wo kwarai mu yi godiya.
Mu yaba mu san ni’ima tasa
Da ya sa suna bisa gaskiya.
Duniya gama duka sai kaɗan
Aka gaji ai mata gaskiya.
Bahari na Kamilu nai a yau
Ya zame abun na yi godiya.
Da kafafuwa duka nasa ne
Iyadiidide duka sun tsaya.
Mu ƙida bahar duka goma sha-
Shida mun tiƙe su gaba daya.
Da guda guda muka kammala
Wakafi a Tilde da safiya.
Mu yi addu’armu ga Rabbana
Salama, tsarin duka anbiya.
Haka ma uwa da uba duka
Haka muslimina gaba daya.
Daga ni Ali haka ma da kai
Ya tsare mu duk mu yi lafiya.
Zunuba duka ya kawar da su
Ya maye su tun daga duniya.
Ayuka duka su tarar da kai
Ka tsare mu duk haɗarin riya.
Rahama ta zam mana ga ta nan
Mu yi hamdala mu yi godiya.
***
Tammat bihamdillah
***