✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanonin sadarwa sun yi asarar masu amfani da data miliyan 1.27

Kudin data a Afirka ya fi ko’ina tsada a duniya

Gasa a kan data a tsakanin kamfanonin sadarwa da ke kasar nan ta ci gaba, inda adadin masu amfani da da data a masana’atar ya yi kasa da kimanin kashi 0.9.

Bayanai sun ce takaddama a tsakanin kamfanonin sadarwa, wato MTN Nigeria da Glo da Airtel Nigeria da kuma 9mobile ta jawo asarar masu amfani da data miliyan daya da dubu 270.

Hakan ta faru ne bayan da abokan hulda suka yi watsi da kamfanonin sadarwar suka rika neman tsarin data da ya fi nasu.

Wani nazari a kan rahoton masana’antar ya nuna babu wani kamfanin sadarwa da ya ci riba a watan Afrilu da Mayu, inda dukkansu suka yi asara a bangaren hannun jarin kasuwancinsu.

Nazarin ya gano cewa Kamfanin Airtel ya fi tafka asara, yayin da 9mobile ya fi karancin asara.

Kamfanin MTN ya kasance jagora a harkar kasuwanci a watan, amma ya yi fama da asara a bangaren data, yayin da Glo ya ci gaba da zama na biyu a hannu jari a kasuwar, gaba kadan da babban mai kalubalantarsa wato Airtel.

Alkalumma sun nuna cewa kudin data a Afirka ya fi ko’ina tsada a duniya, kuma Najeriya ce ta 43 a duniya.

Wannan ya sa masu sayen data a kasar suka ci gaba da shigar giza-gizai a masana’antar domin samun farashin da ya fi sauki.

Tsadar kudin shiga Intanet da rashin ingancin sadarwa ne manyan matsaloli biyu da suke sa masu amfani da data su yi ta fama da matsaloli, kuma daya daga cikin kamfanoni wato MTN ya kare kansa a baya cewa ingantacciyar sadarwar ce take sa data ta rika saurin sauka.

A karshen watan Mayu, Kamfanin Airtel ya rasa abokan ciniki dubu 906 da 669, inda hakan ya sa masu hulda da shi suka dawo mutum miliyan 36 da dubu 120 a cikin wata daya, maimakon mutum miliyan 37 da 20 a karshen watan Afrilu.

Kamfanin MTN ne ya biyo baya wajen asarar a watan, inda ya rasa masu hulda da shi dubu 243 da 203 a watan Mayu, inda masu ciniki da shi suka yiwo kasa zuwa mutum miliyan 60 da dubu 200, maimakon miliyan 60 da dubu 440 a watan Afrilu.

Masu amfani da data a Kamfanin Glo a watan Mayu dubu 118 da 730 ne suka bar kamfanin, wanda hakan ya rage abokan cinikinsa daga miliyan 37 da dubu 710 a watan Afrilu zuwa miliyan 37 da dubu 590 a watan Mayu.

Kamfanin 9mobile, wanda shi ne yake da mafi karancin masu amfani da data a tsakanin kamfanonin, ya yi asara mafi karanci a watan Mayu, inda masu amfani da data suka yiwo kasa zuwa miliyan shida da dubu 210, maimakon miliyan shida da dubu 220 wanda hakan ya nuna ya rasa abokan ciniki 6,594.