✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kamfanonin jiragen sama na Afirka za su yi hasarar Dala miliyan 300 – IATA

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Duniya IATA, ta yi hasashen cewa, kamfanonin jiragen sama da ke kasashen Nahiyar Afirka ciki har da Najeriya,…

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Duniya IATA, ta yi hasashen cewa, kamfanonin jiragen sama da ke kasashen Nahiyar Afirka ciki har da Najeriya, za su tafka hasarar Dala miliyan 300 a cikin shekara mai zuwa.

Shugaban Hukumar IATA, Aledandre Juniac ne ya bayyana haka, yana mai cewa kamfanonin jiragen saman za su tafka hasarar ce, duk da cewa akwai hasashe mai karfi da ke nuna cewa sashin sufurin jiragen sama a duniya zai samu ribar akalla Dala biliyan 35 da miliyan 500 a shekarar ta 2019.

Kodayake, Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Duniya, ba ta fayyace dalilan da za su haddasa wa kamfanonin Afirka hasarar ta Dala miliyan 300 ba, masana na kallon al’amarin da cewa ba zai rasa nasaba da batun tattalin arziki da zuba hannayen jari ba.

Sai dai duk da haka, Hukumar IATA ta yi hasashen cewa shekarar 2019 za ta fi armashi ga kamfanonin sufurin jiragen sama na Najeriya da sauran takwarorinsu na Afirka, bisa la’akari da cewa a shekarar 2018 mai karewa kadai sun tafka hasarar Dala miliyan 400.