Matsalar karancin mai ta tilasta wa kamfanonin jiragen sama a Najeriya dakatar da ayyukansu.
Kamfanonin sufurin jiragen sama sun kara farashin tikitinsu a kwanakin baya.
- Tsohon dan kwallon Najeriya Justice Christopher ya rasu
- Rikicin Ukraine: Romaniya za ta bai wa ’yan Najeriya gurabun karatu
A ranar kamfanonin sun ce sun yi mamakin ganin karin farashin man jirgin sama, inda aka sayar da lita a kan Naira 607 a Kano.
Wannan ya nuna an kara fiye da Naira 100 cikin kwana guda.
Aminiya ta rawaito cewa wasu masu kamfanoni sufurin jiragen sama sun samu sanarwar daga dillalan man a ranar Talata cewa farashin man JetA1 ya karu zuwa Naira 597 a Legas, Naira 599 a Abuja da Fatakwal, da kuma Naira 607 a Kano.
A ranar Litinin an sayar da man a kan Naira 470 ne a Legas, a Kano kuma Naira 495.
Hakan ya janyo tsaiko ga tashin jiragen sama a manya da kananan filayen jirgin sama na Najeriya a ranar Laraba.
Yawancin kamfanonin sufurin jiragen saman sun fitar da sanarwar da ke bayana halin da su ka shiga tara da ba wa abokan fasinjojinsu hakuri.
Fasinjoji a filayen jiragen saman kasar nan sun shiga rusu kan rashin samun jiragen da za su yi jigilarsu.