✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kamfanonin hakar ma’adinai na China na kwace mana filaye – ’Yan Kamaru

Al'ummar kauyen Kambélé da ke Gabashin Kamaru sun koka kan zargin da suka yi wa kamfanonin hakar ma'adanai na kasar China da kwace musu filaye.

Al’ummar kauyen Kambélé da ke Gabashin Kamaru sun koka kan zargin da suka yi wa kamfanonin hakar ma’adanai na kasar China da kwace musu filaye.

Kafar yada labaran Africa News da ke kasar ta rawaito cewa wani mazaunin yankin mai suna George Nabedja, ya ce tun kafin a haife shi mazauna yankin ke hakar gwal.

“Amma tun da mutanen nan suka zo, hakan ya gagare mu.

“Yanzu ba mu isa mu yi aiki a filayenmu ba, saboda sun kwace.

“Da akwai manyan bishiyu saboda daji ne kewaye da mu, amma dubi yanzu ya koma sai ka ce sahara,” inji shi.

Kazalika, a garin Yaounde ma hakan take, domin sun ce suna nadamar yadda zamansu tare da kamfanonin hakar ma’adinai ya dawo.

Wani mazaunin garin mai suna Koumbo Seme Leonard ya ce, “Yanzu ba mu isa mu yi abubuwa yadda muke yi ba a da.

“Kamfanonin Chinan nan sun mai da mu kamar bayinsu, saboda yadda suka takura mana,” inji shi.

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Foder, ta ce ta sha tattaro rahoton yadda ake samun kwacen filaye, sai dai gwamnati ta yi biris da lamarin.

“Wasu jagororin yankin an daure su a kurkuku, don kawai suna kokarin kare gidajensu.

“Don haka a ce wadannan kamfanonin na kasar Sin na zaman ta ci barkatai ne a wadannan yankunan, ba laifi ba ne.

“Amma daya daga cikin abubuwan da ke kara dagula lamarin shi ne rashin tsarin filayen da ake da shi a yankunan.”

Kafar ta Africa News ta kuma ce matsalar na ci gaba da dagulewa, yayin da mazauna yankin ke jiran shiga tsakanin mahukunta da samar da dokokin amfani da filaye.

Kungiyar ta Foder dai ta sha alwashin ci gaba da sa ido  kan yadda al’ummar yankunan ke gidanar da lamuransu.