✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kamfanoni 75 sun nuna sha’awar sayen tituna 12 daga Gwamnatin Tarayya

Akalla kamfanoni 75 ne suka mika bukatarsu ta sayen manyan titunan Gwamnatin Tarayya guda 12 da ake kokarin cefanarwa. Manyan hanyoyin da ke cikin rukuni…

Akalla kamfanoni 75 ne suka mika bukatarsu ta sayen manyan titunan Gwamnatin Tarayya guda 12 da ake kokarin cefanarwa.

Manyan hanyoyin da ke cikin rukuni na farkon da za a cefanar sun hada da hanyar Kano zuwa Maiduguri da Kano zuwa Katsina da Abuja zuwa Keffi zuwa Akwanga da kuma Abuja zuwa Lakwaja.

Sauran sun hada da hanyar da Lakwaja zuwa Benin da Enugu zuwa Fatakwal da Ilorin zuwa Jebba da Legas zuwa Abeokuta da kuma hanyar Legas zuwa Badagry.

Akwai kuma hanyar Benin zuwa Asaba da Onitsha zuwa Aba zuwa Owerri da kuma Shagamu zuwa Benin.

Yunkurin dai na zuwa ne bayan Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta ta ba wa kamfanoni masu zaman kansu damar kula da hanyoyin, karkashin kulawar Hukumar Kula da Manyan Hanyoyi ta Kasa (HDMI).

Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola ya ce daukar matakin a ya zama dole la’akari da yadda Gwamnatin Tarayya ke fama da karancin kudaden da zata ci gaba da kula da sama da kilomita 35,000 na manyan titunanta a fadin kasar.

Sanarwar da Daraktan Watsa Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar, Boade Akinola, ya fitar ranar Laraba, ta ce an gudanar da gwanjon titunan ne ta intanet domin tabbatar da cewar an yi komai a fili.

“An bude shafin na intanet ne domin a karbi bukatar kamfanonin bisa ka’idojin da aka shimfida. Yanzu haka kamfanoni 75 ne suka nuna sha’awarsu ta sayen hanyoyin,” inji sanarwar.

Ta ce dole duk kamfanin da ke son sayen wani daga ciki titunan ya cika dukkannin sharudan da aka gindaya kafin daga bisani a gayyace su domin gabatar da kudirin hakan a rubuce.

A baya dai yunkurin na Gwamnatin Tarayya na sayar da kadarorinta ya sha tayar da kura tare da fuskantar Allah-wadai daga bangarori da dama na Najeriya.

%d bloggers like this: